sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • ALLAH YA GIRMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM HASSAN ASKARI A.S
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • Ubangiji ya faranta muku da haihuwar Imam Ali bn Abu dalib (as)

   

  قال الإمام الصادق(عليه السلام): «كان العباس بن عبد المطّلب ويزيد بن قَعنَب جالسين ما بين فريق بني هاشم إلى فريق عبد العزّى بإزاء بيت الله الحرام، إذ أتت فاطمة بنت أسد بن هاشم أُمّ أمير المؤمنين(عليه السلام)، وكانت حاملة بأمير المؤمنين(عليه السلام) لتسعة أشهر، وكان يوم التمام.

  Imam Sadik (as) yace: Abbas bn Abdul –mudallib da Yazidu bn Ka'anab suin kasance a zaune tsakanin kungiyar Banu Hashim da jama'ar Abdul-Uza kishiya da dakin Allah mai alfarma, sai kawai ga Fatima Bintu Asad bn Hashim mahaifiyar sarkin muminai ta taho tana dauke da cikin Sarkin muminai (as) na wata tara, wannan rana ta kasance ranar karshe ranar da ta haihu.

  قال: فوقفت بإزاء البيت الحرام، وقد أخذها الطلق، فرمت بطرفها نحو السماء، وقالت : أي ربّ، إنّي مؤمنة بك، وبما جاء به من عندك الرسول، وبكلّ نبيّ من أنبيائك، وبكلّ كتابٍ أنزلته، وإنّي مصدّقة بكلام جدّي إبراهيم الخليل، وإنّه بنى بيتك العتيق، فأسألك بحقّ هذا البيت ومن بناه، وبهذا المولود الذي في أحشائي الذي يكلّمني ويؤنسني بحديثه، وأنا موقنة أنّه إحدى آياتك ودلائلك لمّا يسّرت عليَّ ولادتي.

  Sai ta tsaya fuskar dakin Allah mai alfarma, sai na kuda ta kamata sai ta daga kanta sama tace: ya ubangiji lallai ni nayi imani da kai da kuma abinda manzo ya zo shi daga gareka, da dukkanin annabi daga annabawanka, da dukkanin littafin d aka saukar da shi, lallai ni mai gasgata dukkanin kalaman kakana Ibrahim khaleel ce, lallai shine ya gina dakinka, ina rokonka don alfarmar wannan daki da wanda ya gina shi da wannan wanda yake cikin cikina da yake magana da ni yake debe mini hasoda maganarsa, lallai ni mai yakini ce kan cewa lallai shi daya daga cikin ayoyinka ne da dalilanka ka taimaka ka saukake mini haihuwarsa.

  قال العباس بن عبد المطلّب ويزيد بن قعنب : لمّا تكلّمت فاطمة بنت أسد ودعت بهذا الدعاء، رأينا البيت قد انفتح من ظهره، ودخلت فاطمة فيه وغابت عن أبصارنا، ثمّ عادت الفتحة والتزقت بأذن الله (تعالى)، فرمنا أن نفتح الباب ليصل إليها بعض نسائنا، فلم ينفتح الباب، فعلمنا أنّ ذلك أمر من أمر الله تعالى، وبقيت فاطمة في البيت ثلاثة أيّام.

  Abbas bn Abdul –mudallib da Yazidu bn Ka'anab sunce: lokaicn da Fatima bintu Asad tayi magana ta yi wannan addu'a, sai muka gad akin ya bude daga bayansa, sai ta shiga ta buya daga idanuwanmu, sannan wannan tsagewa ta dawo da dinke da izinin Allah madaukaki, sai mukayi yunkurin bude kofa domin `yan'uwanta mata su shiga amma sai kofar ta ki buduwa, sai muka san cewa haka wani al'amari ne daga al'amuran ubangiji madaukaki, ta wanzu cikin wannan daki tsahon kwanaki uku jere.

  قال: وأهل مكّة يتحدّثون بذلك في أفواه السكك، وتتحدّث المخدّرات في خدورهنّ.

  Yace: Mutanen garin Makka sun ta tattaunawa kan haka, wadanda suke cikin haimomi suntan tattauna hakan cikin haimominsu.

  قال: فلمّا كان بعد ثلاثة أيّام انفتح البيت من الموضع الذي كانت دخلت فيه، فخرجت فاطمة وعلي(عليه السلام) على يديها، ثمّ قالت: معاشر الناس، إنّ الله عزّ وجلّ اختارني من خلقه، وفضلّني على المختارات ممّن مضى قبلي، وقد اختار الله آسية بنت مزاحم فإنّها عبدت الله سرّاً في موضعٍ لا يجب أن يُعبد الله فيه إلّا اضطراراً، ومريم بنت عمران حيث اختارها الله، ويسّر عليها ولادة عيسى، فهزّت الجذع اليابس من النخلة في فلاة من الأرض حتّى تساقط عليها رطباً جنياً.

  Yace: bayan kwanaki uku sai dakin ya bude daga inda ua tsage ta shiga, sai ta fito (as) tana dauke da shi a hannunta, sannan tace: yaku taron mutane, lallai Allah Azza wa Jalla ya zabe ni daga cikin halittunsa, ya fifita ni kan zababbun mata daga wadanda suka gabata gabani na, hakika ya zabi Asiya bintu Mazahim lallai ta bautawa Allah a boye a mahallin da baya zama wajibi a bautawa Allah sai cikin larura, hakama ya zabi Maryam bintu Imran ya saukake mata haihuwar Isa (as) sai ta girgiza busashshen kututturen bishiyar dabino a daji har yayi mata yayyafin danyen dabino abin dasa

  وإنّ الله تعالى اختارني وفضّلني عليهما، وعلى كلّ من مضى قبلي من نساء العالمين، لأنّي ولدت في بيته العتيق، وبقيت فيه ثلاثة أيّام آكل من ثمار الجنّة وأوراقها، فلمّا أردت أن أخرج وولدي على يدي هتف بي هاتف وقال: يا فاطمة، سمّيه علياً، فأنا العليّ الأعلى، وإنّي خلقته من قدرتي، وعزّ جلالي، وقسط عدلي، واشتققت اسمه من اسمي، وأدّبته بأدبي، وفوّضت إليه أمري، ووقفته على غامض علمي، وولد في بيتي، وهو أوّل من يؤذّن فوق بيتي، ويكسر الأصنام ويرميها على وجهها، ويعظّمني ويمجّدني ويهلّلني، وهو الإمام بعد حبيبي ونبيي وخيرتي من خلقي محمّد رسولي، ووصيّه، فطوبى لمن أحبّه ونصره، والويل لمن عصاه وخذله وجحد حقّه»

  Lallai Allah ya zabeni ya fifita ni kansu biyun da kan dukkanin wadanda suka gabata gabani na, saboda ni na haihu cikin `yantaccen daki na kuma zauna cikin tsahon kwanaki uku ina ci daga kayan marmarin aljanna da ganyayyakinta, yayinda da nayi niyyar fitowa alhalin dana yana hannuna sai naji wani sauti yace mini ya Fatima ki sanya masa suna Ali (madaukaki) saboda ni ne mafi daukakar daukaka,lallai ni na halicce shidaga kudurata da daukakar buwayata,  da yankin adalcina, lallai na tsago sunansa daga sunana, na kuma ladabtar da shi da ladubbana, na fawwala masa al'amarina na tsinkayar da shi boyayyen ilimina, an haife shi cikin dakina, shine farkon wanda zai fara kiran sallah a saman kan dakina, shine wanda zai karkarya gumaka ya wurgo su kan fuskarsu, ya girmamani ya daga ni ya tsarkake bautata, shine Imami bayan masoyina annabina zababbena daga halittuna Muhammad manzona, kuma shine wasiyinsa, farinciki ya tabbata ga wanda ya so shi ya taimake shi, azaba da bomi su tabbata kan wanda saba masa yaki taimakonsa yayi ja da shi.

  Sayyid Himyari Allah yayi masa rahama yace:

  ولدته في حرم الإله وأمنه ** والبيت حيث فناؤه والمسجد

  بيضاء طاهرة الثياب كريمة ** طابت وطاب وليدها والمولد

  في ليلةٍ غابت نحوس نجومها ** وبدت مع القمر المنير الأسعد

  ما لُفّ في خرق القوابل مثله ** إلّا ابن آمنة النبي محمّد

  Ta haife shi cikin dakin ubangiji da ma'amintarsa** da daki wurin farfajiyarsa da masallaci**fara tasa mai tsarkakakken tufafi karramamma**ta tsarkaku `dan da ta haifa ma ya tsarkaka haifaffe cikin daren shu'umancin taurarinsa ya faku** ta bayyana tareda wata mai haskaka mafi azurta

  Ba a lullube wani mutum cikin zanin unguwarzoma misalinsa ba** face `dan Amina annabi Muhammad.