sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

Ubangiji ya girmama ladanku da namu bisa wafatin Sayyada Zainab diyar Imam Ali bn Abu dalib (as)

 

Haihuwarta:

A haifeta a garin Madina shekara biyar bayan hijira a watan Jimada Awwal, lokacin da aka haifeta (as) mahaifiyarta Zahara (as) ta zo da ita wajen babanta sarkin muminai (as) ta ce masa: sanya mata suna, sai yace ban kasance wand azai gabaci manzon Allah (s.a.w) a daidai lokacin manzon Allah (s.a.w) yayi tafiya, yayin da ya dawo sai Imam Ali (as0 ya tambaye shi kan wanne suna ya sanya mata, sai manzon Allah (s.a.w) yace: ban kasance mai rinjayar ubangijina madaukaki ba, sai take Jibrilu (as) ya sauko yana isar da sakon gaisuwa daga madaukaki mai girma, yace masa: ka sanya mata suna Zainab hakika Allah ya zabar mata wannan sunan, sannan ya bashi labarin abinda zai faru da ita nan gaba daga musibu, sai ya fashe da kuka (s.a.w) sannan yace: duk wanda yayi kuka kan musibar da ta samu wannan yarinya ya kasance kamar wanda yayi kuka kan `yan’uwanta biyu Hassan da Husaini.

 

Tarihin rayuwarta da falalarta:

Ta kasance malamar da bata da malami fahimtatta da ba a fahimtar da ita, mai hankali da zurfin tunani, ta kasance cikin fasaharta da gudun duniyarta da ibadarta kamar misalin babanta sarkin muminai da mahaifiyarta Zahara (as).

Hakika ta siffantu da kyawawan dabi’u masu yawa da siffofi masu girma, da halaye ababen yabawa da tsarkakakkun falaloli, ta rawaito hadisai daga mahaifiyarta hakama daga Asma’u bintu Umaisu kamar yanda Muhammad bn Amru da Adda’u bn Sa’ib suka rawaito hadisai daga gareta, haka Fatima bintu Husaini (as) da Jabir bn Abdullahi Ansari da Ubbadu Amiri, Zainab ta shahara da yawan tahajjudi, sha’aninta cikin haka kamar misalin sha’anin kakanta ne manzon Allah (s.a.w) da ahalin gidansa (as), an rawaito daga Imam Zainul Abidin (as) fadinsa:  

 ( ما رأيت عمّتي تصلّي الليل عن جلوس إلاّ ليلة الحادي عشر ) ،

Ban taba ganin gwaggona tana sallah a zaune ba sai a daren goma sha daya.

Ma’ana ba ta taba barin sallar dare ba da sauran ibadojinta na mustahabbi  hatta wannan dare da yake cike da bakin ciki, ta yanda Imam Husaini (as) lokacin da yayi bankwana da iyalinsa bankwanansa na karshe ranar ashura  yace mata

( يا أختاه لا تنسيني في نافلة الليل )

Ya yar’uwata kada ki manta da ni cikin nafilarki ta dare.

Ba’arin wasu masana sira sun ambaci cewa: Sayyada Zainab (as) tana da wani kebantaccen majalisin Tafsirin kur’ani mai girma da mata suke halarta, lallai addu’arta amsashshiya ce.

 

Ummu masa’ib

Ana mata lakabi da wannan suna, lallai ta cancanci wannan suna, hakika ta ga musibu musibar wafatin kakanta annabi (s.a.w) ta ga shahadar mahaifiyarta Zahara (as) da shahadar sarkin muminai da shahadar dan’uwanta Hassan (as) daga karshe kuma ta ga musiba mafi girma shahadar dan’uwanta Imam Husaini (as) a waki’ar daffi Karbala tareda sauran shahidai (rd)

 

Labarinta a filin karbala:

Hakika Sayyada (as) tana wani bayyananne matsaya a filin karbala cikin dukkanin fagage itace wadda ta dinga bada kulawa ga wadanda suka illatu tana kuma sanya ido kan dan’uwanta Husaini (as) lokaci bayan lokaci tana Magana da shi tana tambayarsa a duk lokaci da wani abu ya faru, itace wadda ta dinga tafiyar al’amuran iyalinsa da kananan yara, ta tsayu cikin hakan matsayar mazaje, abinda yafi jawo hankali shine kasantuwarta a wannan lokaci matar Abdullah bn Jafar amma sai ta zabi bin dan’uwanta maimakon zama tareda mijinta kuma shi mijin ya yarda ta tafi can, hakika ya umarci yayansa biyu da su bi ta suyi jihadi gabanta, wacce take da dan’uwa misalin Husaini (as) tana cikin wannan madaukakiyar kamala, baa bin mamaki na gareta ta fifita dan’uwanta kan mijinta.

An rawaito cewa yayinda ranar sha daya ga watan muharram tayi bayan kashe Imam Husaini (as) Umar bn Sa’ad ya kai hari kan mata ya dbe ya wuce da su ta kan jana’izar Imam Husaini (as) Sayyada Zainab (as) tayi kukan neman taimako kan dan’uwanta.