sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • ALLAH YA GIRMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM HASSAN ASKARI A.S
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
 • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S)
 • ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI KAIWA ABU ABDULLAHI HUSAIN ZIYARA A.S
 • UBANGIJI YA GIRMAMA LADANKU KAN SHAHADAR IMAM HASSAN ALMUJTABA (A.S)
 • Tsokaci dangane da zamanin Imam Alkazim (as

  Image result for ‫موسی الکاظم امام‬‎

   

  Dan takaitaccen tsokaci dangane zamanin Imam Alkazim (a.s))

  Hakika Imamai sha biyu (a.s) daga zuriyar manzon Allah(s.a.w) dukkanin su daga haske daya suka fito hakikar muhammadiya tana tajalli cikin su waton kasantuwar sa rahama ga dukkanin talikai, lallai sun kasance dayantar hadafi da manufa sai dai kowannen su yanada rawar da ya taka mafi girman hadafin su da manufar su shi ne kare muslunci da tsare shi har ya kai lokacin da zai cika duniya da Adalci da daidaito bayan ta cika da zalunci da danniya, duk da banbancin rawar da kowannen su ya taka  cikin isar da sakon Allah da kare shi daga abin da ya kewayu daga yanayin zamani da bukatun sa da yadda yake kasancewa da yanda yake hukuntawa.

  Sai dai ita rayuwar Imam Alkazim (a.s) da halayen sa da sulukin sa masu albarka daga baki dayan sasanni da fagage, lalle rayuwar sa ta fifita ta kuma banbanta da dakiya cikin tsayawa kan gaskiya da kafewa da kuma tsayawa kyam a gaban matsaloli masu ban tsoro a wancan zamani nasa ta hanyar yakar su da kuma mabayyanin suluki da karkacewa bata tasiri cikin sa ko cunuwa da tsoratarwa lallai Imam (a.s) ya siffantu da daidaituwa, hakika zamanin Imam Sadik da Imam Alkazim (a.s) zamani ne da ya cika da afkuwar al’amurra masu ban tsoro da mamaki sakamakon kasantuwar sa zamani da siyasar sarakuna ke tashenta kai Musamman ma motsi da yunkuri da ya kasance dauke da makamai  wanda mafi bayyana da shaharar sa shi ne juyin- juya halin shahidi Zaidu ibn Ali (a.s) da juyin-juya halin Hashimawa wanda ya yi sanadiyar faduwar daular Umayyawa mayaudara, lallai al’ummar musulmi sun yunkura cikin hamasa zuwa ga kawar da daular Umayyawa makiya Ahlul baiti (a.s) wadanda daular su ta kafu kan kaskantar da al’ummar musulmi da zaluntar su da kwace hakkokin su da karamcin su da danne musu mafi kankantar hakki daga hakkokin shari’a da zamantakewa da Abubuwan da rayuwa ta doru kansu wannan juyin juya hali na Hashimawa ya yunkuro da taken yarda na ga iyalan manzon Allah (s.a.w) lallai wannan juyin juya halin ya samu karbuwa daga jama’a  daga kowanne jigawa da kurmi jama’a sun yunkura da hamasa domin karamcin su da kuma kubuta daga zalunci da danniyar Umayyawa bisa imanin su da cewa iyalan manzon Allah (s.a.w) sune tushe na farko domin samun madaukakin hadafi da kowa ke nema da fafutika domin aikata adalci da dabbaka shi da zartar da shi cikin zamantakewa da kuma karfafa `yanci da yaduwar sa da daidaito da bada hakkoki.

  babu wani mutum da ya yi zaton cewa wannan juyin-juya hali na kunshe da yaudara da kawo Banul Abbas kan karagar mulki bayan kawar da Banu Umayya domin su Banu Abbas ma ai tuntuni ambaton su ya dadishe basu da wani shaida abar nunawa ko wani aiki da su ka yi tukuru da zai zama abin misali ga hidimtawa muslunci da musulmai..

  Daga baya sai wannan yunkuri na juyin juya hali ya karkace ya juya daga hanyar da yake kai da aka tsara masa daga garin Abwa’i lokacin da aka yi wa Muhammad ibn Abdullah Zul Nafsul zakiyya mubaya’a ga halifanci ya karkata ga yiwa Banul Abbas mubaya’a da dora su kan karagar mulki da jagorancin Abu Muslim Kurasani bisa wani tsararren shiri da ittifaki na boye da su ka yi a bayan labule da aka yi cikin duhun dare wanda ya kafa turakun mulkin Abbasiyawa da sojojin Kurasan da Bagadaza da Damashak.

  Mulkin Banul Abbas bai kafu ba face kan tafkunan jinane da tulin gawarwaki da suka kashe wadanda cikin su akwai wanda basu da laifin komai basu ji basu gani ba, daga kananan yara da marasa lafiya da tsofaffi.

  Kamar yadda ayyuka na bushewar zuciya da Mansur Abbasi Aldawaniki ya gudanar wanda ya sunnanta su kan `ya`yan baffan sa Alawiyyawa wadda ta tafi ta bar gurbi mai zurfi da radadi cikin zukatan Imamai biyu Sadik da Alkazim (a.s) bayan Mansur Dawaniki ya azabtar da `ya`yan baffanen sa Hassan da Husaini (a.s) da mafi muni da tsananin azaba, daga cikin guraben da sakamako da wannan hari da waki’ar suka haifar shi ne mikewar mulkin danniya da rashin tausayi da kisan daruruwan Alawiyyawa cikin waki’ar (Fakku) da ta afku kusa da garin Makka mai karamci.

  Imam Alkazim (a.s) da kankin kansa ya ga dukkanin wadannan musibu da kashe-kashe masu tsananin `daci da radadi ya kuma dayantu da dauriya da hadiye fushi da yin hakuri da daukar wahalhalu da musibu masu tsanani wadanda ya yi gogayya da su daga dawagitan zamanin sa halifofin zalunci da danniya da fajirci, hakika sun kai iyaka cikin zaluntar sa da azabtar da shi, hakika sarakunan Abbasiyawa sun yi yunkurin halaka Imam Alkazim (a.s) lokuta da dama ta hanyoyi daban-daban Musammam ma Sarki Almahadi da Haruna Rashid wanda daga karshe Haruna Rashid (l.) ya yi gangancin halaka shi bayan ya daure shi ya wurga shi cikin gidan yari da yake cike da duhu cikin ramin rijiya bayan ya kore shi daga garin Madina garin kakansa (s.a.w) ya zuwa Iraki ya tsare shi a birnin Basara daga nan kuma ya mayar da shi zuwa Bagdaza tsawon shekaru Imam (a.s) ya na ta fama da wahalhalu daga wannan sai waccan cikin danne hakkokin sa da zaluntar sa da tsananta masa yanata kwankwadar bala’i da musibu sai dai cewa hakan sam bai tasiri kansa ba cikin kokawa ko yin raki daga wannan radadi mai tsanani, bari ma dai shi ya kasance ya na bayyana godiyarsa ga ubangijin sa domin tsawon lokaci yana rokon Allah ya azurta shi da wani lokaci dai zai bauta masa da yankewa gare shi, kai hatta makiyin sa Haruna Abbasi (a.s) ya yi masa shaida kuma ita falala shi ne abin da hatta makiyinka ya yi maka shaida kansa, lallai shi yayin da aka tsare shi a gidan yarin Falalu ibn Rabi’i shi Falalu ya ba da labarin yadda Imam (a.s) yake yawan ibada da tahajjudi da zuhudu daga duniya da fuskantar ubangiji matsarkaki sai Haruna Abbasi (l.a) ya ce: (lallai babu shakka shi waliyyine daga cikin Banu Hashim) tarihin yadda ya rayu ya kasance yana mallakar zukata lallai cike yake da daukakar ma’anoni da tsarkaka da girma da gudun duniya da tarkacenta da sallamawa zuwa ga Allah mai girma da daukaka.

   

  Cikin gidan yarin Sanadi ibn Shahik da umarnin Haruna Rashid (l.a) aka shayar da Imam Alkazim (a.s) guba mai kisa wadda ta halakar da rayuwar sa da shahadantar da shi yana cikin halin bautar Allah da tahajjudi Amincin Allah ya tabbata gare shi da iyayen sa tsarkaka zababbu mafi falalar gaisuwa da aminci garesu da mafi cikar girma da karamci da hakkin ma’abocin girma da karamci.

   

  Makarantar Imam Alkazim (a.s):

  Idan muka bijiro da wani bangare daga rayuwar Imamin mu majibancin lamarin mu Imam Musa Alkazim (a.s) lalle zamu sami kawukan mu gaban tarin gado mai girma mai cika zuciya mai nutsuwa mai haskaka da take kwarar da alheri da kyawu, tana dauke da kayauta da da fuskanta dadacacciya ga al’ummar musulmi cikin amudan zamani.

   

  Kamar yadda Imamin mu ya tsaya kyam cikin gudanar da lamurran al’umma da suke tattare da ilimin baban sa Sadik (a.s) da kakansa Bakir (a.s) wanda ya tsage ya keta ilimi mutanen farko dana karshe sai ya zamanto ya assasa makaranta madawwamiya da ta ginu kan littafin Allah da zuriyar manzon Allah (s.a.w) zababbu tsarkaka kan hankaltuwa hujjar Allah boyayya wacce ake la’akari da ita a matsayin cibiya ta farko ta wayar da kai da hankali a muslunci, ita ce makaranta ta farko da ta yaye taurari da gaggan malamai daga cikin su sahabbai marawaitan hadisai daga Imamai da kuma Almajiran su, sannan haskenta ya mike tsawon zamanai da suka a baya  ya tuke har zamaninmu dama wanda zai zo baya zuwa bayyanar Imamul hujja (a.f) lallai wannan makaranta na dauke da ruhin muslunci na hakika da shiriyar sa mai albarka madawwamiya da dawwamar Kur’ani da zamani.

  Lalle shi Imam (a.s) da wannan makaranta tasa mai shiryarwa ya yaki matsaloli wanda zamanin sa ya haifar da su sakamakon yaduwar munanan Akidu da tunannuka masu rusa addini kamar misalin zindikanci da gullanci da makamantan su hakika wadannan munanan Abubuwa sun nufi ganin bayan muslunci da girgiza turakun da ya kafu kansu.

  Hakika Imam Musa Alkazim (a.s) ya bugi kirji ya kalubalance su da dukkanin bakin ikon sa da abin da yanayi ya saukaka masa da yake kewaye da shi, kamar yadda mahaifin sa ya yi a baya, ya fito da ilimin sa ya bayyanar da hujjojin sa cikin munazarori da ya yi tare da masu dauke da ire iren wadannan miyagun Akidu da tunannnuka daga gullanci da zindikanci da makamantan su daga tunanunka dake ruguza addini wadanda suka cika duniyar muslunci a wancan lokaci su kai yunkurin tsinka igiyar da ta hada musulmai da dangantakar su ta zamantakewa da kuma batar da ra’ayi gamamme cikin yawancin bangarorin sa na zamantakewa da Akida, lalle Imam (a.s) ya yi gaggawa wajen farkar da musulmai da tsoratar da su hadarin wadancan akidu na bata da karkatar tunani da akida kamar yadda mahaifin sa Sadik (a.s) ya yi a baya.

  Imam (a.s) ya kasance ya gudanar da munazarara mai cike da balaga 

   tare da  yahudu da nasara, kamar yadda ya yi tare da abokan bugawar sa da makiyansa da halifofin zamanin sa, lalle Imam (a.s) ya samu nasara cikin dukkanin munazarorin da tsayar da hujja mai isarwa da dalili mai huda mai ruguje dalilan makiya ya rusa da’awowin su da abinda suka tafi kai, lallai Imam (a.s) ya kasance ya taka bayyananniyar rawa cikin ruguje shubuhohin zindikai da masu kore samuwar Allah da shubuhohin masu bin kagaggiyar mazhaba da makalolin su cikin fagen tauhidi da akidu na gaskiya gasgatattu, haka ya tabbatar da gurbatar Akidun masu kore samuwar Allah da munafukai da kangararru karkatattu.

  Wannan Kenan ballantana sahabban sa da almajiran sa, lallai sun taka rawa cikin yada tunanin Imamanci da bahasinta madaukaki, kamar misalin Husham ibn Hakam  da Hisham ibn Salim da Muminil Daku da sauransu daga sahabban Imamai, hakan duka cikin munazarorin su da kafa dalilan su tare da jagororin mazhabobin muslunci a wancan lokaci, Lamarin da ya kai ga yaduwar tunanin Imamai Ahlul baiti (a.s) da yaduwar hadisan su da falalolin su da hujjojin su da hanyar su madaidaiciya albarkacin hujjojin su da dalilan su masu huda da galaba wanda suka doru kan hanyar da tsarin ilimi da bahasi da yake kan maudu’i tsantsa da tunani `yantacce, da hankali dacacce da wayewa.

  Lallai Imam (a.s) ya wayi gari bayan mahaifinsa Sadik (a.s)  ya zamnto mahaskaka ga ilimi sannan kuma samfurin sanin Allah, ya mike cikin yada ilimummukan Ahlul baiti (a.s) ta hanyar ba da darasi  da muhadara ta ilimi  da rawaitar da hadisai daga iyayen sa da kakaninsa tsarkaka  da kakansa annabin Allah (s.a.w) cikin ilimummuka daban-daban kamar misalign akidu  da Akhlak da fikihu da hadisi da tafsiri da wasunsu daga ilimummuka da fannoni da iliman sanin addini ga daliban sa da almajiran sa da sahabban sa masu daraja.

  Hakika amsa kuwa gaggan malamai masana fikihu da marawaita hadisai masu daraja sun fito daga wannan makaranta wanda adadinsu ya kai mutum (539) masana hadisi da fikihu wadanda malam shabastari cikin littafin (Ahsanul Tarijim Li Ashabul Imam Musal Kazim (a.s) ya kidaito mutum 532 daga cikin wadanda suka rawaici hadisai daga gare shi (a.s) sannan ya riskar da mutum bakwai daga karshen littafin.

  Hakika mutane bakwai daga sahabban sa sun fifitu da gaskiya da rikon amana wadanda dukkanin jama’a da marawaitan hadisai su kayi ijma’I kan gaskiyarsu cikin dukkanin abin da suke rawaitowa daga Imamai tsarkaka amintattu, sannan mutum goma sha takwas sun shahara daga marawaitan hadisai na Imamiya sune wadanda suka shahara aka sansu da sunan Ashabul ijma’i daga sahabban Imamai uku na Bakir da Sadik da Alkazim (a.s) wasu kuma sun ce su sha tarane 19 shida daga sahabban Abu Jafar Muhammadl bakir (a.s)  shida kuma daga Abu Abdullah Imam Jafar Sadik (a.s) shida karshe daga Abu Hassan Imam Musa Alkazim (a.s) sune: Yunus ibn Abdur Rahman, Sufwanu ibn Yahaya Bayya’u Sabiri, Mohd ibn Abu Umairu, Abdullah ibn Mugira, Hassan ibn Mahbub Sarrad, Ahmad ibn Mohd ibn Abi Nasar Albazandi (ks) lalle su sun kasance daga manya manyan sikoki. Wadannan a fagen fikihu Kenan amma ragowar fagagen tunani da akidu (ilmul kalam) da lugga da kur’ani da abin da ya kama da su lalle nan ma akwai zababbu kebantattu ciki.

  An karbo daga Sayyid Dawus (ks) lallai ya kasance idan wasu kebantattun jama’a daga sahabban Abul Hassan Imam Musa Alkazim (a.s) daga Ahlul baiti da `yan shi’arsa suka halarci majalisinsa sannan tare da su akwai Allon rubuntu da yake aljihunan hannun rigarsu, take idan ya furta kalma cikin wani Abu da yake sauka sai su rubuta ta daga abin da sukaji daga gare shi.

  Ahmad ibn Hanbal Limamin mazhabar hanbaliya ya kasance yana rawaita daga Imam Alkazim (a.s) sai ya ce: Musa ibn Jafar ya zantar dani ya ce: baban Jafar ibn Muhammad ya zantar dani ya ce: babana Ali Husaini ibn Ali ya zantar dani ya ce: baban Husaini ibn Ali ya zantar dani ya ce: Abu Husaini ibn Ali ya zantar dani ya ce: babana Ali ibn Abu dalib (a.s) ya zantar dani ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya ce. Sannan Ahmad ibn Hanbal ya ce: da za’a karanta wannan isandi kan mahaukaci da take ya warke daga cutar hauka.

  Daga cikin wadanda suka rawaita daga Imam Musa kazim(a.s) akwai kadibu albagdadi cikin tarihin bagdad, da sam’ani cikin arisala alkawwamiya, da Abu sAlihu mu’azzinu  cikin arba’in, da sa’alabi cikin Alkashfu walbayan.

  Hakika sahabban Imam (a.s) da almajiransa da shi’arsa sun taka rawa mai muhimmancin gaske cikin yada ilimin muslunci cikin dukkanin wani yanki duniya  tsakannin kebantattun da gama gari, hakika makarantar Imam kazim (a.s) ta yaye zababbu fitattu daga malamai manya-manya da masana fikihu da akidu daga cikisu sika mai girman daraja  Hisham ibn Hakam hakika ya kware ya goge cikin ilimin sanin akida  da kuma cikin munazara da jidali har sai da ya shahara tsakankanin masana a wannan zamani, hakika ya rawaici da yawa-yawan riwayoyi cikin akidu da tafsiri da hukunce-hukunce, sannan ya zam ta hanyar munazararsa karfaffa tare da kafirai da masu kore samuwar Allah da zindikai da munafukai da masu mazhabobi sabanin mazhabar Ahlul baiti da ire irensu. Ya kasance yana fitowa daga munazararsa cikin nasara har ta kai ga wasu daga abokan munazararsa suna sallamawa gaskiya su rungumeta su muslunta su riki mazhbar Ahlul baiti (a.s) kamar yadda tarihin da nassoshi sukai shaida kan haka.