sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar shigowa uku ga watan Sha’aban Ranar da aka haifi Imam Husaini a.s

 

 


An haifi Imam Husaini (as) manzon Allah (s.a.w) da kansa ya kasance cikin tarbarsa cikin halin farinciki, bushara ta mamaye sama da kasa, wannan al’amari ya kasance da yammacin ranar alhamis daren juma’a uku ga watan sha’aban a shekara ta hudu da hijirar mai albarka.

Hamawini cikin labarin da ya danganta shi zuwa ga Ibn Abbas yace: lokacin da aka haifi Imam Husaini Allah Azza wa Jalla yayi wahayi zuwa da Mala’ika mai gadin wuta da ya kashe wuta kan wadanda suke cikinta saboda karamcin wanda aka Haifawa Muhammad a duniya. Kakansa Mustafa (s.a.w) ya dauke shi ya rungume shi sannan ya sumbace shi, bayan haka yayi kiransa sallah a kunnensa na dama sannan ya tada ikama a na hagu, ya sanya masa suna Husaini ya yanka masa rago, ya cewa babarsa Fatima (as) ki aske gashinsa ki sadaka da azurfa gwargwadon nauyin gashinsa, a wani fadin ance ya yanka masa akuya ne, ya kuma bada sadaka gwargadon nauyin gashinsa mai albarka.