sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).
 • MURNAR TUNAWA DA HAIHUWAR HASKEN GIDAN MUHAMMADU GUDA UKU
 • ALLAH YA GIRMMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM KAZIM A.S
 • LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
 • MUHADARAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI KAN MURNAR ZAGAYOWAR RANAR DA AKA HAIFI FIYAYYEN HALITTU (S.A.W) DA IMAM SADIK A.S
 • FARA TARON BAJAKOLIN LITATTAFAI NA KASHASHE A JAMI’ATU ALU BAITI A.S
 • RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S
 • ALLAH YA GIRMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM HASSAN ASKARI A.S
 • SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI CIGABA DA BAHASUL KARIJ
 • MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)
 • TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S)
 • Labarun da ba tsammani

  Tunawa da Ranar haihuwar Imam Aliyu bn Husaini Zainul Abidin Amincin Allah ya tabbata a gare shi

  sakonsa zuwa ga shi’arsa da sahabbansa:

  da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

  ni da ku Allah ya isar mana daga kaidin Azzalumaida zaluncin  mahassada, da damkar jabberai, ya muminai kada dawagitai da mabiyansa daga makwadaitan wannan duniya su fitinar da ku, masu karkata ga duniya da nufarta, masu narkewa, ita duniya tarkacenta yana raunana, kayayyakinta gobe suna zama babu su, ku kauracewa abinda Allah ya ja kunnuwanku daga gareta, ku guji abinda Allah ya kwabeku daga cikinta, lallai ita duniya tana daukaka kaskantacce ta kuma tozarta mutum mai daraja, tana kuma gangarar da mazaunanta zuwa wuta, cikin haka akwai abin lura da fadaka da kwaba ga ma’abota fadaka, ke nemi taimakon Allah, ku koma zuwa ga `da’arsa da `da’ar wanda yake mafi cancantuwa da `da’a  daga wadanda suka bi ubangji sai akai musu `da’a.

   

  ayi taka tsantsan ayi taka tsantsan daga fadawa cikin abinda zai kai ku ga nadama da hasara, da zuwa wurin ubangiji da tsayuwa a gabansa, na rantse da Allah babu wasu mutane da suka gangaro daga sabo Allah face sun gangara cikin azabarsa, babu wasu mutane da suka fifita duniya kan lahira face majuyarsu da makomarsu ta munana, ba komai bane sanin Allah da yi masa `da’a face abokan juna biyu da suke hade, duk wanda ya san Allah lallai zai ji tsoransa, tsoron zai kwadaitar da shi kan yin aiki da `da’ar ubangiji, hakika manyan Malamai da mabiyansu wadanda suka san Allah sukai aiki don shi, suka yi kwadayi zuwa gareshi, hakika Allah yace:

   إنما يخشى الله من عباده العلماء»

  Kadai dai masu tsoran Allah daga bayinsa sune malamai.

  Kada ku nemi wani abu cikin wannan duniya ta hanyar sabawa Allah, ku shagaltu da `da’arsa, ku ci ganima kwanakinku na duniya, kuyi sa’ayi cikin abinda tsiranku daga azabar Allah yake ciki, lallai hakan shine mafi karancin cutuwa, mafi kusancin uzuri, mafi kusancin samun tsiranku, ku gabatar umarnin Allah, da `da’ar wanda ya wajbta `da’arsa, tsakanin dukkanin al’amura, kada ku gabatar da al’amuran da suka zo muku daga dawagitai daga duniya, gaban al’amarin Allah da `da’arsa da `da’ar ma’abota al’amari daga gareku, ku sani cewa kufa bayin Allah ne mu ma muna tareda ku, shugabanmu zai mana hukunci a ranar gobe, anan ne inda zaku tsaya ayi muku tambayoyi, saboda haka ku tanadi amsa da zaku bayar gabanin tsayuwar, gabanin tambaya, gabanin bijiro da wurin mai rainon talikai, ku sani lallai Allah baya gasgata makaryaci, ba kuma ya karyata mai gaskiya, baya watsi da uzurin wanda ya cancanci uzuri, bai yin uzuri ga wanda bai cancanci uzuri ba, yanada hujja kan halittunsa da manzanni da wasiyyai, bayin Allah kuji tsoran Allah, ku tashi tsaye cikin gyara kawukanku da `da’ar Allah da `da’ar wadanda kuke jibanta cikinta, sarai mai nadama ya nadamtu cikin abinda yayi barna cikin gefan Allah da abinda ya tozartar cikin hakkokin Allah, ku nemi gafarar Allah ku tuba zuwa gareshi lallai shi yana karbar tuba yana kuma yin afuwa daga munanan ayyuka, kuma ya san abind akuke aikatawa, ku guji abota da masu sabawa Alla, ku guji taimakon azzalumai, da makotaka da fasikai،ku tsoran fitinarsu , ku guji majalisansu, ku sani cewa duk wanda ya sabawa waliyyan Allah, zai fita daga addinin Allah, duk wanda ya kadaita da lamarinsa ba tareda waliyin Allah ya kasance cikin wuta mai ruruwa mai ciye jikkuna da rayukansu suka faku daga barinsu, tsiyatarsu tayi galaba, su matattu ne basu jin zafin wuta, da suna raye da sun dandani radadin zafin wuta, ku fadaku yaku ma’abota hankula, sannan ku godewa Allah kan shiryar da ku, ku sani cewa lallai ku baku iya fita daga cikin ikon Allah zuwa waninta, da sannu Allah da manzonsa da muminai za su ga ayyukanku, sannan zuwa gareshi zaku tashi, ku amfani da wa’azi ku ladabtu da ladubban salihai.

  ــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــــ