sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Maulidin Abul Fadlul Abbas bn Ali (as) and akewa lakabi da Kamaru Banu Hashim mai shayar masu kishi a Karbala

An haife shi a hudu ga watan Sha’aban

Daga cikin lakubbansa akwai: Kamaru Banu Hashim, Babul Hawa’ij, Sakka’u, Saba’u kandara, Kafilu Zainab, Badalul Shari’a, Hamilul Liwa’u, Kabashul Katiba, Hami Azima.... .

Mahaifiyarsa: itace Sayyada Fatima Bintu Hazam Al’amiriya Alkilabiyatu, wacce aka fi sani da Ummu Banin

Imam Ali (as) ya aureta saboda samun Abul Fadlu (as):

An raiwato cewa Imam Ali (as) ya cewa dan’uwansa -Akilu wanda ya shahara da sanin nasabar larabawa, ina neman macen da zata haifi wani sadauki daga larabawa domin in aureta ta Haifa mini `da jarumi, sai ya ce masa, ka nemi Fatima bintu Hazam Alkilabiya Al’amiriya, lallai cikin larabawa babu wadanda suka fi iyayenta jarumta, sai Imam yaje ya aureta sai ta Haifa masa, farkon wanda ta fara Haifa masa shine Abbbas (as) bayansa kuma sai Abdullah bayansa sai Jafar da Usman.

Siffofinsa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:

Abbas ya kasance kyakkyawan namiji kakkarfa yana hawan ingarman doki.


قال الإمام الصادق(عليه السلام): «كان عمُّنا العباس بن علي نافذ البصيرة، صلب الإيمان، جاهد مع أبي عبد الله(عليه السلام) وأبلى بلاءً حسناً، ومضى شهيداً

 

Imam Sadik (as) baffanmu Abbas ya kasance kan basira da tsantsar Imani, yayi jihadi tareda Abu Abdullah ya nuna jarumta ya yi shahada.

Hakika ya kasance shi yake dauke da tutar Husaini (as) wannan babbar tuta babu daukar ta sai sadauki jarumi cikin runduna.