sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Nufus Aliyu bn Musa Arrida (as)
 Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Suldanul Shamsul shumus Abul Hassan Aliyu bn Musa Arrida amincin Allah ya kara tabbata a gareshi.

Shine Imam Aliyu bn Musa Imami na takwas daga A’immatu Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu, sune wadanda Manzon Allah (s.a.w) yayi bushara da su cikin hadisai masu yawna gaske, daga cikinsu akwai hadisi mai daraja da ya zo cikin ingantattun litattafan Ahlus-sunna kuma baki dayan al’ummar musulmai suka ittifaki kansu, sune halifofi goma sha biyu dukkaninsu daga Kuraishawa, a wata riwayar kuma ya zo da lafazin (wasiyyai bayana) (jagorori a bayana) da makamancin haka daga riwayoyi masu tarin yawa,

Ana yima Imam Rida (as) Alkunya da Abu Hassan, sannan ana yi masa lakabi da Arrida, an haife shi a birnin Madina Almunawwara shekara ta 148 da hijira, haka zalika ana yi masa da Garibul Guraba  sakamakon binne shi da akayi a binrin Kurasan a kasar Farisa yana mai nesanta daga kakansa manzon Allah (s.a.w).

Amincin Allah ya tabbata a gareshi ya kasance yana girmama baki, yana cika su da ni’imomi da hidimomi da ihsani, ya kasance yana mike da kansa cikin gaggauta yiwa baki hidima, hakika yayi wa wani mutum liyafa da ya sauka wurinsa , Imam (as) ya kasance yana zantar da shi hadisi cikin ba’arin wasu darare sai fitila da take haskaka su ta lalace sai wannan bako ya yunkura don ya gyara ta sai Imam (as) yayi wuf yayi sauri ya gyara da kansa, sannan ya cewa wannan bako: mu mutane ne bama sanya bakinmu aiki.

Daga mafi soyuwar al’amura wurin Imam (as) shine yaga ya `yantar da baiwa ko bawa daga bauta, marawaitan hadisi suna cewa Imam Arrida (as) ya `yantar da baiwa da bawa dubu.

  Imam (as) ya kasance mutum mai yawan yin ihsani ga bayi, Abdullah ibn Saltu ya rawaito daga wani mutumi daga Balka yace: na kasance tareda Imam Arrida (as) cikin tafiye-tafiyensa  zuwa Kurasan sai wata rana ya sa akawo masa abinci sai ya tattara bayinsa kan wannan abinci wasunsu daga Kasar Sudan da wasu kasashen, sai nace raina fansarka zai fi kyawu ka warewa wadannan abincin daban, sai Imam (as) ya nuna rashin amincewarsa kan wanann shawara yace masa: yi minin shiru rufe mini baki ubangiji tabaraka wa ta’ala daya ne, uwa daya ce, uba daya ne,  shi sakamako yana kasance ne da aikin da aka yi.

Hakika sirar da tarihin tsarin yanda A’immatu Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu suka rayu ya kasance kan hadafin watsi da nuna banbanci tsakankanin mutane, baki dayan mutane sun kasance cikin bautawa ubangiji guda daya, ba’arinsu bai iya fifita kan ba’ari face da tsoran Allah da kuma yin aiki nagari.