sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

TUNAWA DA HAIHUWAR IMAM ALIYU BN MUHAMMAD ALHADI A.S

 

 

 

Imam Aliyu bn Muhammad bn Ali ban Musa bn Jafar bn Muhammad bn Ali bn Husanini bn Ali bn Abu Dalib (as) shine na jerin Imami na goma daga Imaman Ahlil-baiti (as) wadanda Allah ya tafiyar da datti daga garesu ya tsarkake su tsarkakewa.

An haife shi a tsakiyar watan Zul Hijja ko kuma biyu ga watan Rajab shekara 214 da yin hijira, kamar yanda ya zo a cikin Usulul Kafi da Al’irshad da Misbah, a alkaryar Sariya wacce take dan nisan daga birnin Madina Almunawwara.

Ya fito daga gidan Annabta da manzanci shi reshe ne daga rassan Ahlil-baiti wadanda suke kaddin mutumtaka kaddin Muhammad shugaban Annabawa da manzanni (s.a.w) wanda yake kewaye da kulawar ubangiji, Imam Hadis hi da babansa dukkansu ma’asumai datattu daga Allah, ana kira tsarkakkar mahaifiyarsa da sunan Samanatu Almagarabiya.

Ya taso ya kuma samu tarbiyar kur’ani mai girma da dabi’antuwa da dabi’ar Annabi Akram (s.a.w) da ta jikkantu ciki babansa mafi alherin jikkantuwa, hakika ayoyi kaifin basira sun bayyana daga gareshi masu ban mamaki wacce Imami mai girma