sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

UBANGIJI YA GIRMAMA LADANKU KAN SHAHADAR IMAM HASSAN ALMUJTABA (A.S)

UBANGIJI YA GIRMAMA LADANKU KAN SHAHADAR IMAM HASSAN ALMUJTABA (A.S)

Daga cikin zantukansa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:

«إنّ هذا القرآن فيه مصابيح النور، وشفاء الصدور، فليجل جالٍ بصره ،
وليلجم الصفة قلبه ، فإنّ التفكير حياة قلب البصير، كما يمشي المستنير في الظلمات بالنور».

Hakika wannan Kur'ani cikinsa akwai fitilun haske, warakar kiraza, dukkanin mai neman yayewa yay aye idanunsa da shi.

Hakika daga dabi'un Mumini karfi a cikin addininsa, da karamci cikin tausasawa, da zage daura damara cikin ilimi, da yalwatawa cikin ciyarwa, da tsakatsaki cikin ibada, da kauracewa kwadayi da buri, da kyautatawa, da daidaituwa, kuma ba ya aikata zalunci kan wanda yake kiyayya da shi, haka bai aikata saboda soyayya wanda yake so, baya da'awar abinda ba nasa ba, baya jayayya kan hakkin da ya kansa, baya kifce baya yafice baya gulma, zaka same shi yana kushu'i cikin sallarsa , yana yalwatawa cikin zakka, shi mai yawan yabawa cikin yalwa, shi mai yawan hakuri ne lokacin da yake cikin bala'i, yana gamsuwa da abinda yake hannunsa, fushi baya kwadayi cikin ribatarsa, basa hada hanya da rowa, yana cudanya da mutane domin neman Karin ilimi, yana kama bakinsa daga magana domin kubuta, idan aka zalunce shi sai ya barwa Allah.

Amincin Allah ya kara tabbata a gareshi yace:

ما تشاور قوم إلّا هدوا إلى رشدهم .

اللؤم أن لا تشكر النعمة .

العار أهون من النار.

Mutane basu taba haduwa sun yi shawara da juna ba face an shirayar da su zuwa shiriyarsu.

Abin zargi shine ka kasance mara godiya kan ni'ima.

Kunyata itace mafi saukaka daga shiga wuta.

لا تواخِ أحدآ حتّى تعرف موارده ومصادره ، فإذا استنبطت الخبرة ورضيت العشرة فآخه على إقالة العثرة والمواساة في العُسرة .

Ka da kulla `yan'uwantaka da wani mutum har sai ka fara sanin mahallansa da magangararsa, idan ka gano gogewa ka gamsu da mu'amala da shi to ka kulla `yan'uwamntaka da shi a kan zobaitar da tuntube da taimaikon juna lokacin tsanani.

من أدام الاختلاف إلى المسجد أصاب إحدى ثمان : آية محكمة ، وأخآ مستفادآ، وعلمآ مستطرفآ، ورحمة منتظرة ، وكلمة تدلّه على الهدى ، أو تردّه عن ردى ، وترک الذنوب حياءً، أو خشية .

Duk wanda ya yawaita zuwa masallaci zai kacibus da daya daga abubuwa takwas: aya bayyananniya, `dan'uwa mai amfanarwa, barabuwan ilimi, rahamar da ake dako da tsimayi, Kalmar da zata shiryar da shi kan shiriya, ko kuma da kawar da shi daga halaka, da barin aikata zunubi sakamakon jin kunya.

هلاک الناس في ثلاث : الكبر والحرص والحسد، فالكبر هلاک الدين وبه لعن إبليس ، والحرص عدوّ النفس وبه اُخرج آدم من الجنّة ، والحسد رائد السوء ومنه قتل هابيل قابيل

Halakar da kai na cikin abubuwa guda uku: girman kai da kadayi da hassada, girman kai halakar adddini sakamakonsa a ka tsinewa Iblis, shi ko kwadayi makiyin nafsu ne da shi aka fitar da Adamu daga cikin aljanna, hassada ita mummunan jagora ce sakamakon hassada Habila ya kashe Kabila.