sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

ASSAYID ADIL-ALAWI ZAI KAIWA ABU ABDULLAHI HUSAIN ZIYARA A.S

SANARWA SANARWA

Soyayyar Husaini ta haukata ni

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai
{  ذَٰلِكَ وَمَن يُعَظِّمْ شَعَائِرَ اللَّهِ فَإِنَّهَا مِن تَقْوَى الْقُلُوبِ }

Wancananka duk wanda ya raya ibadojin Allah lallai yana daga takawar zukata

Amin Allah ya tabbata a gareka ya Abu Abdullahi Husaini
samahatus Assayid Adil-Alawi zai kaiwa masoyinsa ziyara wato Abu Abdullahi Husaini amincin Allah ya kara tabbata a gareshi zai kai ziyarar ne da kafarsa yana mai tattaki idan Allah ya raya shi ya kuma bashi lafiya da taufikin yin hakan da yardarsa madaukaki.

Zai fara ne cikin kwanakin tattakin zagayowar kwanaki Arba'in da shahadar Imam Husaini a shekara ta 1441 hijri zai tattako daga Najaf zuwa Karbala tareda Majalisin zaman juyayin Husaini (a.s)  da kuma laccoci na Aklak da yardar Allah, za a fara laccocin ne daga masallacin Sahla da yake Kufa bayan idar da sallar Azuhur ranar Laraba 17 ga watan Safar 1441 hijiri