sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S)

TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S)

ذكرى رحيل نبي الامة  وولده الإمام الحسن (ع)

Tunawa da wafatin Annabin Rahama da dansa Imam Hassan (as)

Muna gabatar ta’aziya zuwa ga mukamin Sahibul Asri waz zaman, Imamul Hujjatul Muntazar kan tunawa da shahadar kakanninsa tsarkaka, Manzon Allah (s.a.w) da Imam Hassan Almujtaba (a.s), Amincin Allah ya tabbata gareka ya manzon Allah Amincin Allah ya tabbata a gareka ya wanda aka shayar guba ya wanda aka zlunta, amincin Allah ya tabbata a gareka ya farincikin Manzon Allah (s.a.w) amincin Allah ya tabbata gareka ya shugaban samarin gidan aljanna, amincin Allah ya tabbata a gareka ya shahidi ya mazlumi amincin Allah ya tabbata ga Imam Hassan Ibn Ali (a.s)  

Imam Hassan (a.s) yace:

«بَینَ الْحَقِّ وَ الْباطِلِ أَرْبَعُ أَصابِعَ، ما رَأَیتَ بِعَینَیكَ فَهُوَ الْحَقُّ وَ قَدْ تَسْمَعُ بِأُذُنَیكَ باطِلاً كَثیرًا


Tsakanin gaskiya da karya yatsu hudu ne, abinda ka gani da idanuwanka shine gaskiya ka kan ji karya mai yawa da kunnuwanka.

Manzon Allah (s.a.w)


یا ایها الناس ألا اُخبرکم بخیر الناس جدّاً و جدَّةً؟ ألا اُخبرکم ایها الناس بخیر الناس أبا و أمّا؟ ألا اُخبرکم ایها الناس بخیر الناس عمّاً و عمةً؟ ألا اُخبرکم ای‌ها الناس بخیر الناس خالاً و خالةً؟ ثُمَ قال صلی الله علیه و آله و سلم: الحسن و الحسین، ألا إنّ اباهما فی الجنة و أِمهما فی الجنة و... و هُما فی الجنة و من أحبهما فی الجنة و من أحبّ من أحبهما فی الجنة.


yaku mutane yanzu bana baku labari da mafi alherin mutane cikin kakansa da kakarsa? Yanzu bana baku labari da mafi alherin mutane uba da uwa ba? Yanzu bana baku labari ba yaku mutane da mafi alherin mutane gwaggo da baffa? Yanzu bana baku labari da mafi alheri cikin `yan’uwan mahaifiyansa ba? Sannan yace: Hassan da Husaini, lallai ubansu yana aljanna mahaifiyarsu ma tana aljanna… suma suna aljanna duk wanda yake son su shi ma zai shiga aljanna.

A duba littafin Kashaful Yakini, sh 314, Biharul-Anwar j 36 sh 31. Fada’il sh 119. Irshadul Kulub j 2 sh 430, Amali Saduk sh 437.