sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

MUNA MIKA TA’AZIYA GA DAUKACIN GURGUZUN AL’UMMAR MUSULMI BISA SHAHADAR IMAM ALIYU IBN MUSA ARRIDA (A.S)

 Muna mika ta’aziyya ga daukacin gurguzun al’ummar musulmi bisa shahadar Imam Aliyu ibn Musa Arrida (a.s)

Daga cikin zantukansa amincin Allah ya kara tabbata a gareshi:من «من حاسب نفسه ربح ، ومن غفل عنها خسر، ومن خاف أمن ، ومن اعتبر أبصر، ومن أبصر فهم ، ومن فهم علم ، وصديق الجاهل في تعب ، وأفضل المال ما
 وفى به الغرض ، وأفضل العقل معرفة الإنسان نفسه ، والمؤمن إذا غضب لم يخرجه عضبه عن حقّ ، وإذا رضي لم يدخله رضاه في باطل ، وإذا قدر لم يأخذ أكثر من حقّه ». «ليس شيء من الأعمال عند الله عزّ وجلّ بعد الفرائض أفضل من إدخال السرور على المؤمن »

Duk wanda ya yiwa kansa lissafi yaci riba, duk wanda ya gafala daga aikata yayi hasara, duk wanda ya ji tsoro ya aminta, duk wanda ya fadaku ya basirantu, duk wanda ya basirantu ya fahimta, duk wanda ya fahimta ya sani, wanda ya yi abota da Jahili ya wahala, mafi falalar dukiya itace wadda aka cimma manufa da ita, mafi falalar hankali shine mutum ya san kansa. Mumini idan yayi fushi fushinsa ba zai fitar da shi daga gaskiya ba, idan ya yardantu gamsuwarsa ba za ta shigarsa da shi bata ba, idan ya samu dama da iko ba zai debi fiye da hakkinsa ba, babu wani abu mafi falala wurin bayan sauke farillai daga farantawa mumini