sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

Labarun da ba tsammani

ALLAH YA GIRMAMA LADANKU DA NAMU BISA SHAHADAR IMAM HASSAN ASKARI A.S

Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da ranar shahadar Imam Hassan Al'askari amincin Allah ya kara tabbata a gareshi

Muna mika ta'aziyya zuwa ga Sahibul Asari waz Zaman Al'imamul Mahadi dangane da shahadar babansa Imam Hassan Al'askari tsira da amincin Allah ya kara tabbata a garesu haka zalika muna mika ta'aziyar ga daukacin guruguzun al'ummar musulmi, Allah ya azurta mu da ziyararsu a nan duniya a lahira kuma mu rabauta da samun cetonsu albarkacin Muhammad da iyalansa tsarakaka

Daga cikin zantukansa amincin Allah ya tabbata a gareshi

 قال  عليه السلام :

«لا يعرف النعمة إلّا شاكر، ولا يشكر النعمة إلّا العارف ».

Babu wanda ya san ni'ima sai mai godiya, haka babu wanda yake godiya kan ni'ima face wanda ya san darajar ni'imar

«للقلوب خواطر من الهوى ، والعقول تزجر وتزاد، في التجارب علمٌ مستأنف ، والاعتبار يفيد الرشاد، وكفاک أدبآ لنفسک تجنّبک ما تكره لغيرک من غيرک ».

Zukata na da darsuwa daga son rai, hankula ana kwabarsu ana kuma kara su, tajribobi ilimi ne sabo, fadakuwa tana amfanar da shiriya, ya isar maka ladabi a kankin kanka kauracewa abinda baka son sa ga waninka daga waninka.

«إعلم أنّ للحياء مقدارآ، فإن زاد على ذلک فهو ضعف ، وللجود مقدارآ فإن زاد على ذلک فهو سرف ، وللاقتصاد مقدارآ فإن زاد عليه فهو بخل ، وللشجاعة مقدارآ فإن زاد فهو التهوّر».

 Ka sani lallai kunya tana da iyaka, idan ta wuce wannan mikdari sai ta raunana, kyauta na iyaka idan ta wuce iyakarta sai ta zama barna, tattali yana da iyaka idan ya wuce wannan iyaka sai ya zama rowa, jarumta na da iyaka idan ta wuce wannan iyaka sai ta zama rashin hankali. ش ta wuce iyakarta sai ta zama n idan ta wuce wannan mikdari sai ta raunana, kyauta na iyaka idan ta wuce iyakarta sai ta zama n