sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

RANAR IMAMANCIN SAHIBUL-ASRI WAZ-ZAMAN A.S

 Ranar Imamancin Sahibul Asri waz-Zaman babban idi ga daukacin al'ummar ckin duniya yantattu

Cikin bayyanarsa ma'abocin al'amari da zamani adalci zai yadu a dukkanin fadin duniya mutuntaka zata karfafa tati nasara kan saye-sayen rai da zuciya da zaluncin Ja'irai, sabida haka ya sanya ake la'akari da ranar imamancinsa a matsayin babban idi ga daukacin mutane yantattu da muminai ba tareda banbanci ba.

Dalili kan imamancinsa: nassin daga Annabi da kuma iyayensa Ma'sumai, ismarsa da mu'zujizozinsa kamar misalin bada labarinsa kan dukiyar da take cikin Hamyanu, da tsayin rayuwarsa mai daraja. Da nassin mutawatiran hadisai daga Annabi (s.a.w) da cewa da sannu zai cika kasa da adalci kamar yanda ta cika da zalunci da danniya, ni'imar samuwarsa cikin gaiba kubra kamar misalin samuwar rana ne a bayan girgije, ba da ban samuwar hujja ba d akasa ta nutse da ahalinta, albarkacinsa ake azurta talikai, da samuwarsa kasa da sama suka tabbatu, shine shugabanmu majibancin lamarinmu Imaminmu Almuntazar Sahibul-Asari Bakiyatullahi A'azam Allah ya gaggauta bayyanarsa mai daraja ya sanya mu daga cikin tsarkakan shi'arsa mataimakansa masu tallafa masa masu shahada a gabansa, Amin ya Rabbal Alamin.

اللهمّ إنّا نرغب إليک في دولةٍ كريمة ، تعزّ بها الإسلام وأهله ، وتذلّ بها النفاق وأهله ، وتجعلنا فيها من الدعاة إلى طاعتک ، والقادة إلى سبيلک ، وترزقنا فيها كرامة الدنيا والآخرة.

Ya Allah lallai mu kwadayin daula mai karamci daga gareka, da zaka daukaka muslunci da da musulmai da ita, zaka kaskantar munafunci da munafukai da ita, ka kuma sanya mu daga cikin masu kira zuwa biyayyarka, jagorori zuwa tafarkinka, cikinta ka azurta mu karamcin duniya da lahira