sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa

LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA

Da sunan Allah mai Rahama mai jin kai

Dukkanin godiya ta tabbata ga Sarki Allah kamar yanda dama ya canci hakan tsira da aminci su kara tabbata ga fiyayyen halittu Muhammad da iyalansa tsarkaka.

Bayan bazuwar labarin kamuwar Samahatus Assayid Adil-Alawi da cutar annobar korona (covid-19).

Daga abinda muka ji daga bakin Samahatus Assayid muna sanar da masoya cewa Assayid yana cikin alheri kuma yana samun Karin lafiya kadai dai yana bukatar addu’arku domin tunkude wannan bala’i daga gareshi da kuma `ya`yansu guda uku da suma suka kamu da wannan ciwo na annobar Korona, Alhamdulillahi dukkaninsu suna cikin kulawar likitoci da yardar Allah da kuma tallafin addu’arku zasu warke daga wannan ciwo sannan wannan bala’i zai yaye nan ba da jimawa ba da yardar AllahMuna godiya da dukkanin yan’uwa maza da mata da suka dinga kiramu a waya da aiko da sako domin sanin halin da muke ciki, muna rokon Allah ya basu lafiya da kwanciyar hankali alfarmar Muhammad da iyalan gidansa tsarkaka.

Hakika Samahatus Assayid yana godiya kan nuna soyayyarku ta Imani tsarkakka bakuma zai mance da ku ba cikin addu’a da ziyara.

Ya kuma yi muku wasicci da da karanta zikirin:

(حسبنا الله ونعم الوکيل نعم المولی ونعم النصير)

 

Ku kasance cikin alheri da lafiya wurin Allah shine mai taimako

Ofishin Samahatus Assayid Adil-Alawi-birnin Qum mai tsarki.