sababun labare Labarun da ba tsammani Labarai wanda akafi karantawa
 • Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
 • Fara darasin Hauza a shekara 1442 tareda Assayid Adil-Alawi
 • Sirrin dawwama wani shiri ne daga Assayid Adil-Alawi da yake gudana cikin watan Muharram
 • Ganawar Samahatus Assayid Adil-Alawi da ba'arin `yan'uw adaga Hijaz
 • tsare-tsaren laccocin Samahatus Assayid Adil-Alawi cikin watan Muharram Mai Alfarma shekara 1442
 • Bukukuwan kwanaki goma daga watan Muharram mai Alfarma shekara 1442
 • Watan Muharram Mai Alfarma shekara 1442 wata ne na bakin ciki da kuka
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Bakir (as)
 • Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Jawad Amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya faranta kwanakinku da murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Aliyu Ibn Musa Arrida amincin Allah ya tabbata a gareshi.
 • Allah ya faranta kwanakinku da tunawa da ranar haihuwar Fatima Ma’asuma (a.s)
 • ZA A FARA DARASIN BAHASUL-KARIJUL-FIKHU NA ASSAYID ADIL-ALAWI
 • Takwas ga watan Shawwal tunawa da ranar da Wahabiyawa suka ruguje kaburburan A’imma (a’s)
 • Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Allah ya girmama ladanku da naku bisa shahadar shugaban masu Tauhid Sarkin Muminai Ali amincin Allah ya tabbata a gareshi
 • Muna taya ku murnar zagayowar ranar haihuwar Imamul Hassan
 • Mu’assatul Ihsan Alkairiya wacce take karkashin Majma’ul Tablig wal Irshad ta raba taimakon abinci a watan Ramdan Mai albarka
 • tashar tauraron dan Adam mai suna Anna'im zasu watsa laccar Assayid Alawi
 • watsa laccar Assayid Adil-Alawi kai tsaye daga tashar Alma'aref
 • Labarun da ba tsammani

  Haihuwar Fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi (a.s).

  Muna taya daukaci al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar fatan Raunana Al'imamul Muntazar Mahadi Allah ya gaggauta bayyanarsa.
  Shi hasken rana da ta haskaka duk duniya da abinda yake cikinta* hasken nata ya barbazu cikin fadin abinda ta kewayu kansa*mabubbugarta mafi alherin halittu mai shiryar da ita*kuma Amurtada mafi alherin mutane shine mai bata kariya*sannan da Zahara'u tasowarta take da gudanarta*haka Jikoki biyu Alhassan da Husaini majinginarta shugabanta sannan da tsatso daga mutanen gidan Husaini Salihi bayan Salihi sukai ta biyan bayanta da haske da yake da suke shayar da ita sai wannan rana mai haske ta bayyana babu wani abu da yake iya kusanta gareta*
  da haskenta dukkanin duhu ya gushe* ya shugabana kai ne wannan rana kaine kuma mai kake kewaya da ita* ya Mahadi da Hasken fuskarka ga zukata kake shiryar da ita* da bayyanarka rayuka suke kira zuwa maƙaginsu* ya ubangijin bayi ka gaggauta bayyanar mai kiwon bayinka. 
  Wani yanki daga littafin (Ikazul Na'im fi ru'uyati Imamul Ka'im:
  ya zo cikin hadisin Annabi mai daraja:

   الشريف: قال رسول الله ‘: من لم يعرف امام زمانه مات ميتة الجاهلية ميتة كفر وضلال ونفاق. 
  Manzon Allah tsira da amincin Allah ya ƙara tabbata a gareshi da iyalansa tsarkaka yaace: duk wanda bai san Limamin zamaninsa ba ya mutu mutuwar jahiliyya mutuwar kafirci da ɓata da munacunci. 
  Haƙika duk wanda bai san Imaminsa ba sani na aƙida da imani cikin zuciya kamar misalin sanin Allah da Manzo sa. ya zamana ya san shi a matsayin Imami Halifa da wasiccin Manzon Allah (s.a.w), lallai shi imamanci cigaban Annabta ne cikin bata kariya da katangeta daga tozarta da isar da sakonta tsakankanin mutane haka kuma da ɗabbakata cikin jama'a, kamar yanda annabta ta kasance cigaban tauhidi, duk wanda ya mutu bai san Limamin zamaninsa ba da wannan ma'arifa bai samu dangantaka da shi ba da dangantakar wilaya da imamanci da ɗa'a, matuƙar bai yi aiki da wasiyyar Annabawa da Manzanni ba ballantana aikinsa da wasiyyar Allah ga talikai, babu shakka wanda ya kasance misalin haka haihuwarsa da mutuwarsa zata kasance mutuwar jahiliyya ma'ana mutuwarsa ta ginu kan asasin jahilci koma bayan hankali da ilimi.