sababun labare
- Labarai » muna taya gurguzun al’ummar musulmi murnar zagayiwar ranar haihuwar Sarkin Muminai Aliyu BN Abu Talib amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Muna taya ku murna da farin ciki da haihuwar Imam Muhammad Jawad amincin Allah ya tabbata a gareshi.
- Labarai » Sabon littafi mai suna (Ruhul Inaba fi Tafsiril Du’a Sari’ul Ijaba) wallafar Samahatus Assayid Adil-Alawi
- Labarai » Ubangiji ya faranta kwanakinku bisa zagayowar ranar haihu war Assayada Fatima Zahara amincin Allah ya tabbata a gareta
- Labarai » Munasabar tunawa da nasarar juyin juya halin muslunci a cikin Iran
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » Shahadar Fatima Azzahra A.S
- Labarai » Lokutan shiryye-shiryen Aklak da Akidu na Samahatus Assayid Adil-Alawi da zai kasance a tashar Alkausar ta tauraron `dan Adam
- Labarai » Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar Mauludin Annabi (s.a.w) da jikansa Imam Jafar Assadik (a.s)
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu da tunawa da shahadar Imam Hassan Askari amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa da wafatin Manzon Allah (s.a.w) da kuma shahadar jikokinsa Imam Hassan Almujtaba da Imam Rida (a.s
- Labarai » Allah ya grimama ladanku da namu bisa tunawa da shahadar Imam Hassan Almujtaba amincin Allah ya tabbata a gareshi
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa tunawa shahadar Imam Sajjad (a.s)
- Labarai » Fara darasin Hauza a shekara 1442 tareda Assayid Adil-Alawi
Labarun da ba tsammani
- munasabobi » Muna yiwa sahibuz- zaman ta’aziyar shahadar kakansa imamul Aliyu Alhadi amincin Allah ya kara tabbata gareshi
- Labarai » Majalisin ta’aziyya da zaman makokin shahadar sayyada Fatima zahara (as) tareda halartar shaik muntazar wa’izi da fadilatul Sayyid Adil-Alawi (h) da kuma mawakin Ahlil-baiti Husaini Ammar kinani
- Labarai » Cikin taimakon Allah da talalfinsa Assayid Adil ya fara bada bahasul Karijul Usuli cikin sabuwar Daura a shekara ta 1442 hijiriya
- Labarai » JARIDAR SAUTUL KAZIMAINI MAI FITOWA WATA-WATA ADADI NA 225-226 WANNAN KARAM MA TA KARA FITOWA
- Labarai » Samahatus Sayyid Adil-Alawi (h) zai yi muhadara a masallacin Jami’ul Kabir (Basara)
- Labarai » TUNAWA DA WAFATIN MANZON ALLAH DA DANSA IMAM HASSAN (A.S)
- Labarai » Ranar asabar 14 ga watan Rabi’u Awwal Assayid Adil-Alawi (h) zai cigaba da bada darasin bahasul karij
- Labarai » Muna taya daukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar shugabanmu maulanmu aliyu ibn Muhammad hadi annakiyu amincin Allah ya tabbata gareshi
- Labarai » Labaran silsilar darussam akhlak na samahatus sayyid adil alawi a wanda zai kasance a jami’ar ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata garesu.
- Labarai » LABARIN KAMUWAR SAMAHATUS ASSAYID ADIL-ALAWI (H) DA CUTAR KORONA
- munasabobi » TUNAWA DA HAIHUWAR IMAM ALIYU BN MUHAMMAD ALHADI A.S
- Labarai » SABUWAR SHEKARAR MUSLUNCI 1441 TARE DA DAWOWA KARATU DAGA RANAR ASABAR 14 GA WATAN MUHARRAM
- munasabobi » Muna taya daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Imam Jawad (as)
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » Allah ya girmama ladanku da namu bisa shahada wafatin Assayida Zainab diyar Sarkin Muminai amincin Allah ya tabbata a gareshi
Labarai wanda akafi karantawa
- munasabobi » Ma'asumiyya Haura'u Zainab amincin Allah ya kara tabbata gare ta tare da Alkamin-samahatus sayyid Adil Alawi
- Labarai » Imam mahadi(af) da tsawon rayuwa a binciken sabuwar mahanga-tareda alkalamin sayyid adil alawi
- Sanarwa » Bude Bajakoli na litatafai na duniya karo na bakwai
- Labarai » Litatafan da aka buga
- Labarai » Sayyid Adil Alawi ya halarci wurin karatun Al’qurani
- Labarai » An wallafa mujallar kazimain me lamba 204/205 na watan rajab da shaaban na shekaran 1437H wanda yayi dai dai da shekaran 2016
- Labarai » SIRRIN RANAR ASHURA
- Labarai » juyayin wafatin sayyida zainab Alkubra
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Labarai » Sakon ta'aziyya
- Sanarwa » Majallr Kausar ta futo a ranar daya ga Jimada aUlan a shekara ta 1436 Hijira ta kunshi abubuwa kamar haka
- Labarai » al-umar musulmi murnar haihuwa ta Fatima Azz
- Labarai » jan hankali ko fadakarwa ga masu wa'azi
- Sanarwa » Matsayin ilimin Manzan Allah da kuma iyalan gidansa
- Lacca » Fatima zahara madubin kyawun Allah girmansa ya girmama
Baki’a: wani wuri ne tsarkakke a cikin birnin Madinatul Munawwara kusa da masallacin Annabi mai daraja da Kabarin Manzon Allah (s.a.w) cikin wannan Makabarta akwai Kaburburan Imamai (a.s) guda hudu, sune Imamul Hassan Almujtaba, Imam Aliyu Zainul-Abidin, Imam Muhammad Albakir, da Imam Jafar Assadik amincin Allah ya tabbata garesu baki dayansu,
Ta’addanci Alu Sa’ud:
Bayan Alu Sa’ud sun kwaci mulki sun dare kan karagarsa sun mamayi birnin Makka da Madina da garuruwan da suke geffanta a shekara ta 1344 hijiri, sai suka fara tunanin samun wani uzuri da dalili da zasu fake da shi kan ruguje Makabartar Baki’a da goge kufaifayin Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu da Sahabbai, sakamakon suna tsoran irin fushin da zasu fuskanta daga musulmin da suke zaune a yankin Hijaz da sauran dukkanin kasashen musulmai sai suka nemi fatawa daga Malaman Madina kan haramcin gina Kabari.
Suka rubutu neman fatawa babban Alkalin Alkalan Wahabiyawa wanda ake kira da Sulaimanu Ibn Bulaihid ya dauki wannan takardar neman fatawa ya kaita wurin Malaman Madina, da farko ya fara shirya zama da Malamai ya tattauna da su daga karshe saboda barazana da tsorata su da yayi dole Malaman Madina suka sanya hannu kan fatawa da haramta gini kan Kaburbura.
Sakamakon wannan fatawa sai Alu Sa’ud da suke kan karaga suka riki wannan jawabi na neman fatawa matsayin abinda zai halasta musu ruguje Kaburburan da suke Baki’a, wannan ta’addanci nasu a hakika wulakanci ne ga iyalan gidan Annabi (a.s) da samun haka sai kuwa sojojin Wahabiya suka gaggauta rushe wadannan muhallan masu tsarki suka daidaitasu da kasa suka munana kyawunsu suka barsu yashe dabbobi da mutane su takesu, sannan suka sace kayayyakin da suke ajiye na tarihi a cikin makabartar daga shimfidu da hadayoyi da abubuwa masu daraja da wasunsu, suka mayarada wurin kai kace kungurmin daji da fako babu komai ciki, bayan yaduwar labarin ruguje wadannan Kaburbura sun fuskanci mummunan tofin ala tsine da Allah wadai daga al’ummar musulmi daga baki dayan duniya an kuma la’akari da wannan aiki na su matsayin babban laifi da ta’addanci da ya munanawa Waliyyan Allah da kuma kokarin rushe darajojinsu (a.s).
Jaridar Ummul Kura bugu na 69 a 17 ga watan Shawwal shekara 1344 ta kawo nassin neman fatawar da amsar kanta, kai kace dama an tanadi wannan amsa domin karfafa ruguje Makabartar, Jaridar ta kawo Tarihin fitowar fatawar 25 ga watan Ramadan shekara 1344 hijiri, domin shan jinin musulmi da bakanta musu, sai dai cewa akasarin ra’ayin musulmi bai nutsu da wannan uzuri na fatawa ba, an samu fatawowi daga kasashe daban-daban da suka kalubalanci waccan fatawa da cewa ta sabawa shari’ar muslunci.
Ban san inda Malaman Madina suka samo fatawar hana gini kan Kabari ba da kuma wajabcin ruguje shi gabanin zuwan Wahabiya? Me ya sanya suka kame bakinsu suka yi shiru tsawon karnoni tun farkon muslunci kan gini kan kabari gabanin bullar wahabiyawa.
Ashe Kaburburan Shahidai da Sahabbai basu kasance ginannu ba?ashe wadannan wurare basu kasance wuraren ziyara ga ma’abotansu ba? Misalin wurin da aka haifi Annabi (s.a.w) da inda aka haifi Fatima (a.s) da Kabarin Hauwa da Kubba da take samansa, yau ina Kabarin Nana Hauwa’u? ashe kabarinta bai kasance wata karantacciyar hadaya tsaraba ba da yake nuni da shiryarwa kan mace ta farko da ta fara mutuwa a tarihin duniya ? yau ina masallacin Sayyadi Hamza a cikin garin Madina da maziyartarsa da ya kasance? ina wuri kaza ina wuri kaza?
Kur’ani da gina Kaburbura:
Da zamu duba Kur’ani Mai girma a matsayinmu na Musulmi da tabbas zamu ga cewa Kur’ani yana girmama Muminai yan karramasu da gini kan Kaburburansu- wannan wani sanannen al’amari ne tsakankanin al’ummu da suka gabaci bayyanar muslunci-Kur’ani yana zantar da mu Kissar Ashabul Kahfi yayinda aka gano labarinsu bayan shudewar shekaru 309 bayan tauhidi ya rigaya ya yadu yayi galaba kan kafirci.
Tareda haka sai muka samu mutane sun kasu zuwa kashi biyu, wani kaso yana cewa: kuyi kansu wani gini da zai dawwamar da ambatonsu, wannan kason Kafirai, daidai lokacin da muke samun Muminai wadanda irdarsu tayi nasara suna kira da a gini masallaci kan kogon kusa da Kaburburan domin wurin ya zama wata cibiya da bautar Allah da dayanta shi.
Da gina masallaci kan Kaburbura ko kusa da su ya kasance wani abu da yake alamta shirka me ya sanya Musulmai Muminai zasu bada shawarar aikata shi?! Me ya sanya Kur’ani ya kawo wannan shawara tasu ba tareda nakadi da suka kanta ba?! Shin hakan ba zai kasance dalili kan halascin ginin ba
قَالَ الّذِينَ غَلَبُوا عَلَى أَمْرِهِمْ لَنَتّخِذَنّ عَلَيْهِم مّسْجِداً
Wadanda suka yi galaba kan al’amarinsu suka ce zamu riki masallaci a kansu.
Wannan goyan baya da zartarwa daga Kur’ani yana nuni kan ingancin shawarar da suka bayar ta gina masallaci- kuma tabbataccen abu ne cewa tabbatarwa da goyon baya da ya zo daga Kur’ani hujja ne a shari’ance.
Lallai wannan yana shiryarwa kan cewa al’adar Muminai masu tauhidi a baki dayan duniya ta kasance tana gudana kan gina Kabari, kuma suna la’akari da shi matsayin girmamawa ga wanda yake kwance cikin Kabarin, da kuma neman albarka daga abinda Allah ya bashi daga matsayi mai girma, saboda haka ne aka gina wurin kuma Kogon As’habul Kahfi ya zamanto cibiyar girmama da mutunci.
wannan kyakkyawar al’ada bata gushe tana nan a raye hatta cikin zamanin da muke ciki ana girmama Kaburburan manyan mutane masu daraja da Sarakuna, shin akwai wasu mutane mafi daraja da dawwama daga zuriyar Manzon rahama (s.a.w) wadanda Allah ya tafiyar da dukkanin kazanta da datti daga barinsu ya kuma tsarkake su tsarkakewa.