mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Shin wannan riwaya ta inganta

Salamu Alaikum
Ya zo cikin riwayar Imam Kazim amincin Allah ya tabbata a gareshi cewa ya kasance a cikin Banu Isra’ila akwai wani mutumi Mumini da yake da wani Makoci Kafiri, wannan Kafiri ya kasance yana tausayi Mumini yana kyautata masa a zamantakewarsu ta duniya, lokacin da wannan Kafiri ya mutu sai Allah ya gina masa gidan tabo a cikin wuta wannan gida yana kareshi daga zafin wuta sannan arziki yana zuwa gareshi daga wajen wuta, aka ce masa wannan shine abin nan da kake baiwa makocinka.
... Ganin amsa

Tambaya dangane da ayar muwadda

Salamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuhu
Akaramakallahu Allama Assayid Adil-Alawi (H)
Ina da wasu `yan tambayoyi gameda ayar muwadda, ayar da manya daga malamai misalign Saduk su kayi la’akari da ita matsayin dalili kan wajabcin soyayyar Ahlil-baiti amincin Allah ya tabbata a garesu, daidai loakcin da muke samun wasu manya daga Malamai misalin Allama hilli hakama Allama Tabataba’i na wannan zamani suna cewa ayar ta tattaro dukkanin zuriyar Annabi (S.A.W) bawai kadai Ahlil-baiti ba , muna neman Karin bayani daga gareku menene ake nufi daga soyayyar makusanta yaya fadadar soyayyarsu ta zurfafa sannan shine wannan wajabcin soyayya wajabcine na Aklak ko kuma na menene
... ... Ganin amsa

Shin zamu iya tattaro dukkanin addini su zama addini daya

Salamu Alaikum Samahatus Assayid
Assayed zamu iya hado dukkanin addini kan addini daya?
... Ganin amsa

Shin isma da debe tsammani suna haduwa a wurin Annabawa

Ta yaya za ayi ace Annabawa su hada wadannan abubuwa ina nufin ma’asumanci tareda debe tsammani da zato wadanda aka ambace su cikin aya mai daraja a kaur’ani mai girma.
حَتَّى إِذَا اسْتَيْأَسَ الرُّسُلُ وَظَنُّوا أَنَّهُمْ قَدْ كُذِبُوا جَاءَهُمْ نَصْرُنَا فَنُجِّيَ مَنْ نَشَاءُ وَلَا يُرَدُّ بَأْسُنَا عَنِ الْقَوْمِ الْمُجْرِمِينَ
Har Lokacin da Manzanni suka debe tsammani suka yi tsammani an karyata su sai taimakonmu ya zo musu sai mu tseratar da wanda muka so kuma ba a mayar da azabar mu daga mutane Mujrimai.
... Ganin amsa

Yaya Allah ya kallafawa mutane soyayyar iyalan Annabi

Salamu Alaikum
Na farko: Ta kaka Allah ya dora soyayya iyalan gidan Annabi (a.s) kan mutane tareda cewa soyayya bata daga cikin ayyukan da gabbai suke yi da taklifi yake hawa kansu
Da umarni da hani sabida suna da bayyanannun abubuwa sabida haka Allah yace ( ba zaku taba iya adalci tsakankanin mata) ma’ana cikin soyayya?
Na biyu akwai wata shubuha: lallai Annabi da Sarkin Muminai da yayansa Hassan da Husaini amincin Allah ya tabbata a garesu tsawon rayuwarsu basu iya gina al’umma mai soyayya da wilaya a garesu ba sabida hakane ma lokacin waki’ar Karbala babu wanda suke fita tareda Imam Husaini (a. ... ... Ganin amsa

Tura tambaya