mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

RIWAYA DA ISNADINTA ZUWA GA MANZON ALLAH (S.A.W)

Salamu Alaikum akwai wata riwaya da ake ambata ake dangane isndinta ga Manzon Allah (s.a.w) yace: mumini yanada labule dai`dai` har guda 70 idan ya aikata zunubi sai labule gud aya kece daga gareshi, amma idan ya tuba sai Allah ya dawo masa da shi tareda guda bakwai, idna kuma yaki tuba ya kafe kan aikata zunubi da sabo sai baki dayan labulayen su kekkece ya wayi gari babu lullubi da labule gareshi, Allah yayi wahayi ga Mala’ikunsa ku suturce bawana da fukafukanku, lallai shi `dan Adam basa canjawa sai dai su tozarta, ni kuma ina canjawa bana tozartarwa, ... ... Ganin amsa

SHIN ZAMU GA ASSAYADA FATIMA (A.S) A CIKIN ALJANNA

Salamu Alaikum ranar kiyama zamu iya ganin Sayyada Fatima ko Sayyada Zainab amincin Allah ya kara tabbata a garesu ko wasunsu daga matayen gidan Annabta da tsarki mu gansu kan karagun gidan aljanu muna kallon juna ko kuma dai zamu hango su ne daga nesa-nesa ba zamu cudanya da suba.
Muna neman Karin bayani daga wurin Akaramakallahu
... Ganin amsa

INA SON MALAM YAYI MINI BAYANI WANNAN RIWAYA DA ZATA ZO A KASA


Salamu Alaikum
Ina fatan Akaramakallahu zai mini bayani a sharhin kan wannan riwaya shin akwai wata duniya da waninmu ya sameta
Shaik Saduk cikin littafinsa (Attauhid sh 277)
... Ganin amsa

BAYYANA KA’IDA KO INGANTACCEN MINHAJI CIKIN MU’AMALA DA RIWAYOYIN AHLIL-BAITI (A.S) DA SUKA ZO CIKIN LITATTAFAN MALAMAN HADISANMU


Salamu Alaikum
Ina fatan zaku yi mana bayani wata doka ko ka’ida da ko minhaji ingantacce cikin mu’amala da riwayoyin Ahlil-baiti (a.s) da suka zo cikin littafin malaman hadisanmu.
Minhaji na farko: dukkanin riwayoyi sun ingantattu ne har sai rashin ingancinsu ya tabbatu da dalilai
Minhaji na biyu: dukkanin riwayoyi ababen shakku ne har sai ingancinsu ya tabbatu da dalili,
Muna fatan Assayid zai gaya wacce minhaja ce cikin yafi inganci?
Allah ya dawwamar daku cikin kiyayewarsa da kariyarsa.
... Ganin amsa

SHIN ANNABI MUHAMMAD (S.A.W) IMAMI NE


Ya zo cikin ba’arin riwayoyi cewa Annabi Muhammad (s.a.w) ya kasance Imami a lokacin Adamu yana tsakankanin ruwa da yunbu da tabo ko kuma mu ce kasa ma’ana dai gabanin wannan duniyar, sai dai cewa kuma mun samu sai da ya kai ga cika shekarun 40 a aiko masa da sako matsayin manzo, to a yaushe ne ya samu mukamin Imamanci? Mene ne ra’ayin su Akaramakalallahu kan wannan batu?
... Ganin amsa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tura tambaya