mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

RIWAYA DAGA HISHAM IBN HAKAM CIKIN LITTAFIN AL’IHTIJAJ

Salamu Alaikum, riwaya daga Hisham Ibn Hakam cikin littafin Al’ihtijaj wani Zindiki ya tambayi Imam Abu Abdullahi amincin Allah ya kara tabbata a gare shi: yaya Hurul Aini matar aljanna zata kasance cikin duk sanda mijinta ya zo matai ta budurwace? sai yace: lallai ita an halicce ta daga tsarki aibu zai zakke mata wani ciwo bai cudanya da jikinta wani bai keta raminta haila bata kazanta domin babu abinda yake jikinta sai magudanar fitsari. ... Ganin amsa

DAME ZAMU KAFA DALILI KAN WANDA YAKE FADIN CEWA DALILAN DA MUKE KAWO WA KAN MAFI CANCANTUWAR AHLIL-BAITI A.S DALILI NE MARA KARFI

Salamu Alaikum masu sabani damu suna bijire mana da dalilai guda biyu
Na farko: jumlar riwayoyin da muke kafa dalili da su kan marja’iyyar Ahlil-baiti amincin Allah ya kara tabbata a garesu wadanda suka kasance riwayoyi ne daga hanyar Ahlus-suuna dama basu da inganci kwata-kwata musammam ma hadisul Saklaini da ya zo da sigar (littafin Allah da tsatsona matukar kuka yi riko da su ba zaku taba bata ba bayana har abada) kune fa kuke sanya sharadin ilimi da yakini cikin sanin Imami.
... Ganin amsa

DANGANTAKAR MARTABOBI TSAKANIN ALLAH DA SARKIN MUMINAI


Shin dangantakar martabobo tsakanin Allah ta’ala da Sarkin muminai martabobin na Allantaka kadai, ina martabobin ubangijintaka shin Sarkin Muminai yana tarayya da Allah ta’ala cikinsu?
Samahatus Assayid Adil babban malamin addini Allah ya dawwamar da inuwarsa.
Salamu Alaikum wa Rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu.
Tambaya ta abinda Allama Assayid Abdullahi Shubbar Allah ya jikan rai ya ambata cikin littafin Masabihul Anwar fi Halli Mushkilat Akbar juz 2 sh 319 hadisi na 171 abinda aka rawaito daga cikin fadinsa:... ... Ganin amsa

SHIN AKWAI WATA KAIFIYA TAKAITACCIYA LA’ANA DA SALLAMA DA SUKE ZIYARAR ASHURA


Samahatus Assayid Adil-Alawi Allah ya daukaka makaminka ya datar da kai soyayyarsa da kusanci mu kuma ya tabbatar da mu kan hanyar gaskiya lallai shi mai ji mi amsawa ne.
Shin akwai wata takaitacciyar kaifiyar karanta la’ana da sallama da suka zo cikin ziyarar Ashura? Shin karantawa sau daya yana wadatarwa musammam idan ya kasance da niyyar neman biyan bukata?
Musammam da yake mu dalibai ne kuma kololuwar abin da muke so shine samun yarda Allah zukatanmu su rataya da turakun Al’arshin mai girma…ko za ku taimaka mana da wani wuridi da ya dace da mu muna godiya gareku.
... ... Ganin amsa

INA BUKATAR KU KOYAR DANI IRFANI DOMIN IN SAMU KUSANCI ZUWA GA UBANGIJINA


Ina son ku koya mini wani darasi na Irfani wanda ta hanyar sa zan samu kusanci da ubangijina in gudu daga zunubai na baki dayansu in koma ga Allah
... Ganin amsa

Tura tambaya