mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Shin an tsarkake Annabawa (as) daga aikata zunubi

Ka kawo mini ingantacciyar riwaya guda daya rak kan cewa Annabawa ma’asumai ne da isma mudlaka! Sannan su ma Annabawa tsarkakakku ne daga zunubi kamar Ahlil-baiti (as) ... Ganin amsa

Shin ceton manzo zai tsaya iya kan wadanda yake alaka da su ta jini kadai

Shin duk wanda yake da alaka da Ahlil baitin manzon Allah (s.a.w) hisabin da za ai masa ranar kiyama ya banbanta da wanda bai da wata nasaba ta jini da su? Shin manzon Allah (s.a.w) zai ceci duk wanda yake da dangantaka da shi ta jini? ... Ganin amsa

Shin Mahadi yana dora hannun sa kan kawunan bayin Allah


Salam Alaikum
riwayar nan da ta kawo batun cewa Imam Mahadi (as) yana dora hannun sa kan mutane shin tana nufin hankulan mutane zasu samu kammaluwa da kuma barin aikata sabo, ko kuma dai babu tilashi cikin Daular Imam Mahadi (as) ba a tilasa mutane saboda wasu suna cewa shaidan da biyewa son yana wanze har a lokacin daular, shin yana nufin Kenan sabo zai kauce daga samuwa ba tareda tilasawa ba daga bangaren Imam kan sai sun bar aikata sabo?
... Ganin amsa

Aikata zunubi bai fitar da mumini daga imanin sa shin wannan riwaya ta inganta

Salamu Alaikum, manzon Allah (s.a.w) ya ambaci cewa: babu wani bawa da zi fadi ( la’ilaha illallahu) ya mutu a kan haka face sai ya shiga aljanna ko da kuwa yayi zina yayi sata, ko da kuda yayi zina yayi sata, ko da kuwa yayi zina yayi sata, lallai koda Abu Zarruy baya so, sannan an karbo daga gareshi (s.a.w) yace: babu wani zunubi da yake fitar da mumini daga imanin sa, kamar yanda babu aikin ihsani da yake fitar da kafiri daga kafirci, shin wannan riwaya ta inganta, idan ta kasance ingantacciya to me yasa ake samun wata riwayar take karo da ita da ma’anar ta ke bayyana cewa duk wanda ya aikata aiki kaza lallai za a cire imanin sa zai kuma dawwama a wuta , ... ... Ganin amsa

Meye ingancin isnadin hudubar Imam Ali (as) ta 55 daga Nahjul BalagaSalamu Alaikum. Hakika ina cikin damuwa sakamakon gazawa ta ga baiwa daya daga abokan amsa yayin da ya tambaye ni kan ingancin huduba ta 55 da cikin yazo cewa (hakika mun kasance tareda manzon Allah (s.a.w) muna yakar `ya`yanmu da iyayen mu har zuwa dai karshen hudubar) ku taimaka mana da amsa Allah ya kara muku ... Ganin amsa

Tambayoyin da akafi karantawa

Tura tambaya