mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Naso neman Karin bayani daga gareka kan azkar wanda kayi ishararsu cikin littafin ulumul garbiyya

Salamu alaikum
Ina rokon Allah madaukaki mai girma da ya kara maka ilimi da haske alfarmar habibul Mustafa (s.a.w) sayyid ina kaunar neman Karin bayani da tambayarka gameda azkar wadanda kayi bayaninsu da ishararsu cikin littafin ulumul garbiyya misali duk wanda ya karanta ya muhaiminu kafa 125 lallai badininsa zai tsaftata zai kuma tsinkayi hakikanin abubuwa, shin wannan zikiri za a karantashi gwargwadon 125 sau daya a rana ko kuma duk duk sanda yinin ya mika sai a karanta 125 asuba 125 azuhur 125 magariba 125 sai natija tafi sauri.
... ... Ganin amsa

Ta yaya zan samu malamin tarbiya cikin suluki da tarbiyyar irfani

Salamu alaikum
Ina yawan karance karance game da irfani ya bayyana cewa lallai ya zama larura gareni in fara suluki kan tsare-tsare sannu-sannu, tare da cewa ni na amfanu sosai, shin zaku iya taimaka mini don in fara ta hanyar wani malami ko da kuwa ta hanyar aiko da sako na yanar gizo (email) musammam da yake ni ina zaune kasar kanada (Canada)
... Ganin amsa

Menene magani da mafita daga rashin samun aikin yi da rashin karbuwa wajen mutane tare da cewa ni lazimci wasu ayyukan ibanda na mustahabbi cikin neman arziki kamar misalign neman arziki


Salamu alaikum sayyid mai girma
Menene mafita kan rashin aikin yi da rashin karbuwa wajen mutane da toshewar arziki tare da cewa ni din nan na lazimci wasu ayyukan ibada na mustahabbi wajen neman arziki misalin sallar neman arziki wacce hallararku kuka ambaceta daga annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata gareshi da iyalansa tsarkaka da kuma azkaru masu yawan gaske da riwayoyi wadanda duk na karantasu daga littafai da aka rawaito su daga ahlil-baiti (as) amma tareda haka yanayin yana nan yadda yake a baya babu abinda ya cnaja ko ya sauya bari ma dai kullum sai kara tabarbarewa yake yi ... ... Ganin amsa

Shin akwai wani aiki na ibada da zai kai mutum ya zuwa samun wata daraja da cimma muradi

Salamu alaikum
Fiye da shekaru goma na haramtu daga samun mukamin aiki an farlanta wasu sharudda wadanda sukai kamada abinda dama ya fi karfin ikon bil adama shin ko akwai wasu ayyukan ibada da zasu isar dani zuwa ga samun daraja da cimma burina kebantacce tabbas haramtuwarmu daga samun Karin matsayi da daraja ya haifar mana da haramtuwa Karin albashi aiki.
Allah ya saka muku da alheri alfarmar kakarku fadima (as) kada kuyi mana rowar falalar da Allah ya kwarara muku.

... Ganin amsa

Harkokin samun abinci na da arziki na sun tsaya cak sun tabarbare me ya kamata in yi?Salamu alaikum
Na saurareka cikin daya daga muhadarorinka na bidiyo kana yin nasiha kan yin sallar neman arziki, lallai ni na lazimci wannan sallah da ka yi nasiha da yinta tun lokaci mai tsayi tsawon shekaru amma tare da babu abin da ya ce cikin tabarbarewa harkokin samun abinci na, kamar yadda lallai ni na lazimci ayyukan ibada masu tarin yawa kamar misalin ziyarar ashura da yaaita istigfari da karanta kur’ani da yin salloli kamar misalin sallar kun fayakun da sallar jafarul dayyar da sallar istigasa bil hujja cikin kowanne daren alhamis da juma’a karkashin sama kai hatta yin ... ... Ganin amsa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tura tambaya