mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Na gaji daga halin da `dana abin tausayi yake ciki ta yadda `kananan yara ke masa isgili basa kwadayin yin wasa tare da shi ina rokon samahatus-sayyid ya nusantar da ni zuwa ga warwarewa ina sa ran Allah zai yaye mini wannan matsala


Na gaji daga halin da `dana abin tausayi yake ciki ta yadda `kananan yara ke masa isgili basa kwadayin yin wasa tare da shi ina rokon samahatus-sayyid ya nusantar da ni zuwa ga warwarewa ina sa ran Allah zai yaye mini wannan matsala.

amincin Allah ya tabbata ga bawansa na gari sayyid adil-alawi Allah ya dawwamar maka da fairorinsa
sayyid lallai ni `daya daga cikin `ya`yanku ne daga garin kadif saudiya ina rubuto muku wannan wasika tawa ba wai ina nufin kai karar Allah ba Allah ya tsarkaka daga haka, bari dai don neman taimako da fuskantarwa daga gareku cikin wasu al’amura guda biyu:
... ... Ganin amsa

Zikirin ya hayyu ya `kayyum adadi nawa ne ake wuridinsa shin kun bamu izinin yi daga hallararku


Assalamu alaikum sayyid zikirin ya hayyu ya `kayyum guda naa wane ake wuridinsa shin zamu samu izinin yinsa daga gareku, wassalam.
... Ganin amsa

Fasalina bai da kyawu saboda haka ne ma babu wanda ke zuwa neman aure na wannan tunani ya na sanya ni tsanar kaina lokuta da daman gaske, saboda haka ina neman nasiha daga gareka don daina wannan tunani.


Fasalina bai da kyawu saboda ne ma babu wanda ke zuwa neman aure na wannan tunani ya na sanya ni tsanar kaina lokuta da daman gaske, saboda haka ina neman nasiha daga gareka don daina wannan tunani.
Salamu Alaikum
Ni budurwa ce matashiya wacce wasu lokutan na kanyi tunanin cewa fasalina bai da kyawu saboda haka ne ma babu wanda ya zo neman aure na wannan lamari yana sanya ni yawan tsanar kaina. Na kan ji kaina cewa ni kaskantacciya kasan wani na ina zargin ubangijina kan hakan a kowanne lokaci, ina bukatar nasiha daga hallararku don daina wannan tunani.
... ... Ganin amsa

Shin akwai wani hirzi (tsari) ko wani abu makamancinsa da zamu iya sanya shi a mahalli don kariya daga masu kambun baka?

Shin akwai wani hirzi (tsari) ko wani abu makamancinsa da zamu iya sanya shi a mahalli don kariya daga masu kambun baka?
Assalamu alaikum: Allah ya karbi ayyukanku sayyid,

Muna son bude wani mahalli don saye da sayarwa amma muna tsoran masu kambun baka da mahassada shin akwai wani abu da zamu rike shi hirzi (tsari) ko dai wani abu da zamu rubuta shi mu sanya shi a mahallin don kariya da tsari daga mahassada da masu kambun baka?
Mu na rokon addu’arku sayyid.
... Ganin amsa

Zuciya ta tana cikin bukatar magani daga magungunan da kake wasicci da domin ta samu galaba kan waswasi da raye-rayen shaidani (l’a)

Zuciya ta tana cikin bukatar magani daga magungunan da kake wasicci da domin ta samu galaba kan waswasi da raye-rayen shaidani (l’a)
سلام عليكم ورحمة الله وبركاته
Salamu alaikum
Lalle ni na saurari daya daga cikin laccocinka da kayi a watan ramalana mai albarka gameda zuciya, sannan na saurareka shekarar da ta gabata a wata tashar tauraron d`an adam lokacin da kake cewa malamai sune likitocin zukata.
zuciya ta tana da bukatar magani daga magungunan da kake nasiha da komawa garesu domin zuciya ta tai galaba kan waswasi da raye-rayen shaidani, ... ... Ganin amsa

Tura tambaya