mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Menene shafa’a {ceto

Shafa’a tana nufin ceto ko taimako wadda Annabawa da manyan bayin Allah nagari zasuyi da izinin ALLA ga mutuman daya cika sharidda

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai,


Amsa daga Sayyid Adil Alawi

Shafa’a tana nufin ceto ko taimako wadda Annabawa da manyan bayin Allah nagari zasuyi da izinin ALLA ga mutuman daya cika shariddan ta,misali kamar mutuman da yake hawa dutse sai kafar shi tazame to sai wanda yake taradashi ya taimaka masa domin kada ya zame ya fado, to idan mai karatu yafahimci wanna to ga misalinta idan mutum yakasance a rayuwar shi ta duniya muminine wato yayi imani da Allah da manzansa da ranar lahira dasauran shikashikan Musulinci amma sai yazamo yana aikata zunubai to sai ranar kiyama lokacin sakamako saiya sami kanshi ladan shi bai karasami shi ba domin ya shiga aljana to sai Allah yabawa annabawa ko manyan bayin shi dasu cecesu.

Kamar yadda yazo a cikin litatafan mu cewa harma annabawa suma suna jiran ceto na Annabi Muhammad tsira da amuncin Allah ya tabbata a gare shi da iyalin gidan sa.kamar yadda malamai suka nuna ita shafa’a kyautace daga Allah mai girma ,kumar yadda yazo a hadisi cewa akwai wasu aiyuika da suke sakamakon su shafa’ace misali kamar wani hadisi da aka rawaito daga Imamu Rida {A S} yanacewa duk wanda ya ziyar ceni,duk dacewe gidan yana da nisa to ni da iyayena {wato imamai zamu ceceshi ranar gobe kiyama.

Kuma kamar yadda malamai dayawa sunyi rubutu dayawa akan shafa’a, inafatan mai tambayar zai bibiyi abun dasuka rubuta.

Alhamdulillah

 

Tarihi: [2015/4/5]     Ziyara: [854]

Tura tambaya