mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Adduar nemar aure da farincikiah

Sayyid ina bukatar addu’a agare ku don neman samin miji na gari me tsoron Allah wanda zan bashi dukka nin zuciyata kuma na kasance mata ta gari a gare shi me yi masa biyayya kuma uwa me kyautata wa yayan ta.

Da sunan Allah me rahama me jin kai

Assalamu alai kum

 Da irin wannan siffofi da ki zaiyano ya kamata kisan cewa duk lokacin da ka kasance ka ba da kan ka akan wani abu alokacinne wahalhalu da hidimomin wannan abun zai rataya a wuyar ka, na farko kenan

Na biyu: idan Allah ya dau Alkawari baya sabawa ga duk wanda ya kasance bawansa na haqiqa kuma baya rufe masa kofofin sa. Kuma ya kan sanya masa mafita a duk wani matsalolin da ya sami kansa aciki ga duk wanda ya sadaukar da kansa ga Allah, sannan a yawaita yin addu’o’I da kuma tawassuli don neman Allah ya bude miki kofofin

Na uku: gadan wani tsokaci da zan miki shine ya kamata kisan kanki sosai wato kisan ke wa cece, akwai wata ruwaya da take cewa duk wanda ya san kansa, ya san uban gijin sa, kuma duk wanda yasan uban gijin say a san komaim to abin da ya fi dacewa shine ya kamta kiyi hisabi wa kanki. Neman cewa kina so ki kasance mace tagari ga mijin daman Allah ne ke sanya soyayya da kuma qauna a zukatan ma aurata don haka a yawaita rokan sa don samin nasara, ko da kin sami kanki a ko wace irin hali na zaman takewar aure ya kamata ko ta hakuri,  da kuma yawaita addu’o’I da istigfsari da kuma neman ya fiya agun Allah, insha Allah da ikonsa zaki sami sauki acikin rayuwar auren ki.

Yawaita yin addu’o’In  bayan sallar asuba da kuma na bayan sallahr maghriba, domin yin hakan yakan kawo  farinciki da kwanciyar hankali kuma lokacin da ake yawaita karban addu’o’I da kuma biyan bukatu.

والله المستعان

Tarihi: [2016/8/8]     Ziyara: [1875]

Tura tambaya