mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Neman Karin Aure

Assalamu alaikum
Ina da mata da kuma yaya sun kai hudu sanna ina rayuwa cikin kwanciyar hankali, na hadu da wata yarinya wacce na bata shekara sha’uku muna da alaka na aure mutu’a amma sai yakasance muna samun yan wasu matsaloli da ga bangaren mu biyu, gashi na kasance ina sonta sosai kuma itama tana sona menene shawarar ku akan wannan hali da muke ciki?
Sannan ina bukatan istihara daga gare ku akan auren mu

 Da sunan Allah me rahama me jin kai

Idan har yarinyar ta kasance budurwace toh dole a nemi iznin mahaifi, amma abin da yafi muhimmanci ka kokarta ka rike auren ka da kake dashi agida,

Kar kacuci su don biyan bukatar ka na sha’awa, zaka iya samin irin wannan alaka da matar ka ta gida kamar yadda yazo a fadin imam Ali (as) cewa: abin da yafi dace shine kayi aure na da’imi domin ka sami zuri’a na gari.

Sannan shi kuma istihara daga farkon yana da sauki amma daga karshe za ayi na dama.

والله المستعان


Tarihi: [2016/9/8]     Ziyara: [551]

Tura tambaya