mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

AMSAR DA SAYYID ADIL ALAWI BAYAR GA D.R MOHD AYYASH KUBAISI

Hakika wadannan tambayoyi sun kasance suna yimin kai kawo cikin kwakwalwata sai dai kuma kash abin takaicin shine bazan iya amsasu su ba saboda haka Zuwa ga sayyid adil alawi hakika sayyid wadannan tambayoyi ina neman taimako daga Allah da gareku domin samun amsar wadannan tambayoyi.
Tambayoyin sun kasance kan tunawa da shahadar imam husaini(rd) 1-2
Dokta mohd ayyashi kubaisi.
Jaridar al’arab/27 oktoba 2015
Mutum biyu daga musulmai basu da sabani kan falala da darajar da matsayin imam husaini a wurin kakansa manzon Allah(s.a.w) ya isar masa falala da daraja shi da dan’uwansa kasantuwarsu shuwagabannin samarin gidan aljanna kamar yadda ingantaccen hadisi ya tabbatar da hakan wanda tirmizi da ahmad ibn hanbal da wasunsu suka rawaito.
Haka bugu da kari wani hadisin ya siffanta su da cewa sune furen da annabi ke kamsasa da shakar kamshinsu anan duniya kamar yadda buhari da wasunsa suka rawaito.
Haka babu sabani cikin kasantuwar cewa shi husaini an kashe shi bisa zalunci sannan kuma hakika makasansa sun tabe da tozarta da kunyar duniya ga kuma zunubin lahira, ibn taimiya yana cewa: shi husaini Allah ya kara masa yarda hakika an kasheshi bisa zalunci sannan kuma shahidi ne, lalle babu shakka da kokwanto kan kasantuwar kisan husaini na daga cikin mafi girman zunubi sannan wanda ya yi kisan da wanda ya yarda da kisan sun cancanci ukubar Allah.
Sai dai cewa abin da ya kamata a fadakar kai shine yadda tarihi ya saka wannan al’amari na kisan husaini, shi kisan husaini ya faru bayan kisan halifofi uku daga hulfa’u rashidin(halifofin shiriya) sune umar usmanu aliyu, da kuma kisan sahabbai biyu daga cikin sahabban da akaiwa bushara da gidan aljanna ma’ana dalha da zubair, da kuma wani adadi daga muhajirun da ansar Allah ya kara yarda dasu baki dayansu, shin hankali zai karbi cewa mu yiwa dukkanin wadannan kashe kashe da suka afku kallo na gama gari da bai da banbanci da abubuwan da suke faruwa yau da kullum basu da wata alaka da siyasa ko wata manufa? shin wanene abin tambaya kan wadannan kashe kashe? Me yasa suka dinga faruwa a jere daya bayan daya tun bayan faduwar daular farisa ta kisra musammam gashi ta’addanci na farko na kashe umar ya kasance a hannun mutumin da ya fito daga wannan daular ta farisawa wato abu lu’u lu’u farisi majusi wanda kasar iran ta daga darajarsa da girmma shi har a wannan zamanin da muke ciki ana ziyartar kabarinsa, me yasa da muslunci ya ci nasara ya bude yaman ta tabbatu da samun zaman lafiya, haka da akai fatahu sham ta tabbatu, akai fatahu misara ta tabbatu ? amma kuma kasar iraki da iran wadanda suka kasance karkashin ikon daular kisra su basu tabbatu ba.
Yaya zamu fassara dukkanin garuruwan da sahabbai sukai fatahinsu misalin abu ubaida da kalid ibn walid wadanda suka bude sham, haka ma misalin amru ibn asi da ya bude kasar misra, da abu ayyubul Ansari da shi kuma ya bude kasar turkiya in banda kasar iraki wadda dar da da rana a bayyane zakai tajin sautin masu tsinewa sahabbai da sukai fatahun kasashe kai hatta gabanin kisan husaini da kisan mahaifinsa aliyu ibn abi talib, hakika sa’ad ibn abi wakas ya kasance wanda yaci nasarar bude kasar iraki shi kadai ne wanda ya kasance ya bude iraki amma kuma irakawa basu yi maraba da shi bari ma dai sun kai kararsa gurin umar da tuhumar cewa bai kyautata sallah kamar yanda hakan ya zo cikin buhari da wasunsa, har ta kai gashi umar din ya kwabe shi Allah ya kra musu yarda su biyun, umar ya yi hakan don toshe kofar fitina, lalle sa’ad ya kasance dan’uwa ga manzon Allah ta bangaren mahaifiya sannan ya kasance daga na farko farkon muhajirun yana kuma daya daga cikin mutum goma da akaiwa bushara da aljanna tun daga nan duniya. Sannnan abun lura anan shine cewa wannan kara da mutanen iraki suka kai wajen umar kan sa’ad ta kasance ba lokuta da dama bawai sau daya ba wadda ita wannan kara ta kasance ne bayan hare hare masu zafi da sa’ad ibn abi wakas ya jagoranta kan iyakokin daular farisa, saboda ribar kwabe sa’ad ibn abi wakas ga wa ta ke komawa Kenan?
Bisa siyakin tsarin taswirar garuruwa da kasashe masana tarihi sunyi ittifaki kan cewa husaini ya fito daga madina zuwa makka gabanin ya tafi karbala, wannan wata nukuta ce mai jan hankali, ita madina ta kasance mafi kusa zuwa karbala daga makka, sannan abin da masana tarihi dukkansuke fadi shine cewa husaini ya tafi makka domin neman mafaka da aminci bayan watsinsa da kin yin mubaya’arsa ga yazidu ibn mu’awiya sannan ya kasance ya yi shawara da mafi alherin sahabbai daga cikinsu abdullahi ibn umar da abdullahi ibn abbas da Abdullahi ibn zubair da abdullahi ibn jafar da dan’uwansa Muhammad ibn ali wanda akewa lakabi da muhammadu hanfiya(rd) dukkaninsu sun bashi shawara da yi masa nasiha da ya yi zamansa a garin makka ka da ya je garin iraki, sun ankarar da shi daga yaudara muatnen kufa har ibn abbas ke ce masa: hakika idan suka kira zuwa ga yaki lalle babu aminci gareka daga su yaudareka da karyata ka da saba maka su kunya taka su juya su zama mafi tsananin mutane kanka.
Lokacin da husaini ya kafe ya dage kan sai ya fita sai y ace masa (idan ka kasance sai ka fita to kada ka tafi da matayenka da kananan yara lalle ni ina jin tsoro kada a kasheka kamar yadda aka kashe usmanu(rd) alhalin matayensa da `ya`yansa kananan na kallo a a gabansu ana kashe mahaifinsu.
Amma abdullahi ibn umar hakika ya tunatar da husaini kan matsayar mutanen iraki kan mahaiafinsa,inda yake ce masa: (ka tsaya kayi tunani kai kanka kaga yaudarar mutanen iraki da abin da mahaifinka ya dinga fuskanta daga garesu) ya yi da ya fuskanci kafiyar husaini da tsayawa kan sai ya fita sai ya rungumeshi ya fadi shahararriyar kalman nan(na baiwa Allah ajiyarka daga kisa.
Daga cikin misalin ire ire nasihohin da sukaiwa husaini itace nasihar abdullahi ibn zubair inda yake ce masa (ina zaka tafi shin zaka je wajen mutanen da su kasha babanka suka kori dan’uwanka)
Hakika husaini ya fita daga madina zuwa makka sannan kuma daga makka ya fuskanci karbala babu wanda ya taba shi da ace umayyawa nada niyyar kisansa da sun kashe shi kan wannan doguwar hanya kasantuwar garin makka da garin madina na karkashin hukumar yazidu da ikon gwamnoninsa, sannan matsayar husaini kan yazidu bayyane take ba boye ba sannan dukkanin wannan kai komo da husaini yake ba zai yiwu ace ta buya daga idanun yaran yazidu ba, to meye sirrin cikin kai kawo da husaini ke tayi ckin garuruwa yadda ransa ke so ba tareda wani ya taba shi ko cutar da shi sannan babu wanda ya yi tsageranci zubda jininsa sai mutanen karbala? Sannan me yasa y adage ya kafe kan kin zuwa wajen yazidu bayan yazidun ya nemi hakan daga gareshi?
Hakika mafi alherin wanda zai iya bamu wannan amsa shine husaini da kankin kansa bisa dogaro da abin da shaik mufid ya nakalto a littafinsa mai suna al’irshad sh 241 wanada shi mufid ya kasance daga jiga jigan malaman shi’a.
(Imam husaini cikin addu’arsa yana cewa: ya Allah idan ka jiyar da su dadi zuwa wani lokaci to ka tarwatsasu tarwatsawa, ka watsa su ka sanya su datsatstsun hanyoyi, ka da ka taba yardar musu da shugabanni har bada, hakika sun gayya ce mu domin su taimakemu sai suka juya kanmu suka kashemu )
Ga kuma jumlar da sukaina diya ga husaini kansu inda take cewa: (ya ku mutanen kufa ya taron mayaudara da munafunci hakika kun maraitar dani tun ina yarinya karama kun maraitar dani ina babba, kun kashe babana da kakana da baffana da dan’uwana da mijina, kai tir daku tir da makircinku. Ibn kasir juz 8 sh 230, gabaninsu husaini yana cewa cikin wata mukarana mai zurfi: (wadannan mutane suna raya cewa wai yan shi’a na ne sun nemi kasha ni sun kwashe dukiyata wallahi in riki alkawali daga mu’awiya in kare jinina in aminta cikin iyalina shi yafi alheri daga su kasheni su wulakantar da iyalina, da zan yaki mu’awiya da su zasu shaki wuyana su mikani gareshi) kitabul ihtijaj juz 2 sh 10.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

dana na kaina mai neman sanin gaskiya da hakikanin al’amari hakika abin da mai ambaton tarihi ya Ambata kadai ba wani abu bane face jinkirtaccen al’amari daga tarihi  wanda malaman tarihi yaran sarakuna da yan kanzagin halifofi da sarakuna daga umayyawa da abbasiyawa kamar yadda dama a dabi’ace yake cewa za su rubuta abubuwan da sarakuna da halifofin zalunci da danniya ke so, musammam ma da yake ma akwai yunkurinsu na wanke zalincin da sukai  da barnarsu da danniya kan al’ummu da Imani da muslunci, saboda haka ba zai yiwu a iya dogaro da tarihin da alkalaman da aka dauke haya aka biya su kudi suka rubuta ba da ya kasance jinkitacce na jabu.

Ya isar maka zama shaida cikin fadin mai fadi  (da kashe mutane biyu da akaiwa bushara da aljanna) cikin abin da ke wajen mutane na cewa anyiwa mutane goma bushara da aljanna sai dai cewa daga cikin abind ke nuni kan karyata wannan hadisi shi ne abin da ya afku daga kisan wadanda suka warware alkawali lalle manzon Allah(s.a.w) ya baiwa sarkin muminai ali(as) labari cewa da sannu zai yaki  masu warware alkawalima’ana masu warware alkawalin mubaya’a  wanda hakan karara na nuni da ishara kan zarginsu domin shi aliy na tareda da gaskiya kuma gaskiya na tareda shi  duk inda ya juya gaskiya nan take juyawa, duk wanda suka yaki ali lalle sun kasance munafukai lalle su azzaluma, sannan babu shakka cikin kasancewa azzzalumi da munafuki cikin wuta kamar yadda nassi mabayyani ya tabbatar da hakan da kuma nassin kur’ani cikin ayoyi masu tarin yawa, bayan haka ta yaya dalha da zubair wadanda an kashe su suna masu yakar ali (as) zasu kasance daga cikin wadanda akaiwa bushara da aljanna ?  sannan shima ali (as) ace yana daga cikin wadanda akaiwa bushara da aljanna wannan na daga tufka da warwara ace azzalum da wanda aka zalunta da wanda ya yi kisa da wanda ya kashe ace dukkaninsu suna aljanna kuma dukkaninsu suna kan gaskiya da Imani?

Bari dai dole daya cikinsu ya kasance mumini dayan kuma ya kasance munafuki hakan idan sun kasance daga musulmai, sannan su munafukai yan wuta ne  bawai ai musu bushara da aljanna ba  wanda haka na nuni sun aminta daga aikata sabo, subhanallah kuna nufin kuce shaidan da adamu dukkaninsu suna aljanna dayansu tubabbe mai biyayya ga Allah daya kuma mai sabo mai tsaurin kai? Me ya same kune kaka kuke hukunci ko dai kuna canja abubuwa daga hakikanin yadda suke kunewa hankulan musulmai dariya bisa dogaranku ga kagaggun hadisai  da basu da hakika wadanda suka sabwa hakikani da haskakakkun hankula wadanda dukkanin wadannan agaggun hadisai sun kasance kirkirar banu umayya? Abun ban mamaki daga mai Magana shine ace ya yarda da bangare biyu wanda ya yi kisa da wanda aka kashe, ali da abokin rigimarsa, lalle Allah bai sanya zuciya biyu cikin mutum guda zuciya da take yarda da Ali(as) a daya gefen wata zuciyar da take yarda da abokin rigimarsa  daga masu warware alkawali da azzalumai da `yan tawaye, subahanallah wane irin kwakwale wadannan kangaggu da basu gane gaskiya da banbance ta da sanin hakika.   Wannann wacce irin kiyayya ce da gaba kan iran, me yasa wannan kagaggen bincike da bayani bai zoba  gabanin faduwar gwamnatin rida sha gabanin juyin juya hali? me yasa baku kiran iran da majusawa sai bayan faduwar  rida sha fahalawi haka bakwa danganta iraniywa da `yan shi’a da mabiyan abu lu’u lu’u duk sai bayan faduwar rida sha, wai duk mai ya kawo wannan bata suna da boye gaskiya.

Sannan menene wadannan fatahohi da kake ta ambata? Ina tabbatuwa take da zaman lafiya a kasar yaman hakikanin abin da ke faruwa a yaman na karytaka, sannan ina tabbatar da zaman lafiya a sham (siriya) tareda dukkanin abubuwa da ke faruwa cikin sham, ina zaman lafiya da tabbatuwa cikin misra a wannan zamani da muke ciki? Ya subhanallah gashi dai yanzu a wannan zamani a zahairi karara muna kallon zaman lafiya cikin iran sabanin kasashen larabawa hakama babu zaman lafiya cikin mjalisin taimakekeniya na kasashen larabawa, Allah ya kunyataku da wannan bincike da tahalili da yake cike da kabilanci da bangaranci, lalle ita gaskiya duk yadda girgijen kiyayyarku da gaba da jahilci da tsaurin kanku ya sai ta kasance mai bayyanar da kanta rana bayan rana kan duhahhen  girgijenku da tsaurin kanku da gabarku lalle ita gaskiya tana karyata ku.    

(جاء الحق وزهق الباطل إنّ الباطل كان زهوقاً).

Gaskiya ta zo karya ta bushe lalle ita karya ta kasance mai bushewa.

Dama ace zama sallama cewa iraki da kasar farisa basuyi maraba da wanda sukai fatahinsu ba sa’ad ibn abi wakas wanda ya kasance uba ga umar ibn sa’ad Allah ya ninka tsinuwarsa kansa wanda ya kashe imam husaini shugaban shahidai wanda ya yi kisan ne da umarnin mai gidansa yazidu ibn mu’awiya `yan wutar hawiya dacewa shi sa’ad wai sun kai kararsa gun umar kan cewa bai kyawunta sallah to hakan ma na nuna kaifin basirar irakawa da wayewarsa daga kabilar ashuriyin da babiliyin tareda abubuwan da suka rataye guda bakwai, ta yaya za suyi maraba da mutumin da bai kyawunta ginshikin addininsa wadda itace sallah wadda ida ta karbu to ragowar ayyuka ma sun karbu idan kuma akai watsi da ita to ragowar ayyuka ma shikenan anyi watsi da su, lalle hakan na nuni da daukakar saninsu da wayewarsu bawai basu yi  maraba da wanda ya yi fatahin kasarsu me ya sameku ne kaka kuke nazarin tarihi? Idan ya zamanto haka kake karanta tarihi da nazarinsa to sai muma mu ce muma haka muke karanta tarihi kuma hakan ya fi kusa da hakikar yadda abubuwa suke da daidai, mai karatu fadakakke mai kaifin basira ya isar mana zama alkali tsakaninmu shi zai zabi da rinjayarwa cikin kaddarwarku da tamu ba tareda ya yi amfani da gabataccen hukunci ko kabilanci ko bangaranci ba.

Sannan me ya kawo yin alfahari da cewa wai shi dan’uwan mahaifiyar annabi ne lalle ni zan kawo maka `da ga manzon Allah(s.a.w) wanda Allah ya cewa wannan manzo wannan `da bai daga `dansa, ba kowa bane face nuhu dattijon annabawa, saboda haka gaskiya iotace ma’auni ba wai dangantaka ba ranar da babu wata dangantaka tsakaninku, sannan babban misali ai ga baffan annabi kaco kam ma wanda shi yafi kusanci gareshi daga dan’uwan mahaifiyarsa wanda sai muka ga ayar kur’ani gaba daya ma ta zarge shi cikin fadinsa madaukaki: (hannaye biyun abi lahabi sun tabe shim ya tabe) idan kunce ai shi abu lahabi mushrkine to shima gogan naku ai munafukine wanda shi munafuki yana can kasan wuta, saboda haka matsayi da dangantaka basu ne ma’auni ba, kadai dai mafi karamcinku wurin Allah shine wanda yafi tsoron Allah a cikinku.

Saboda abubuwa da mai tankade dai rairaya cikin tarihi ya fada ba kasance bakin komai sai dai jahilicinsa daga tarihi ko kuma tsaurin kai da jirkita hakika, abin da ya zo da shi daga tarihi tarihi ne da hukuma suka biya ladan rubutunsa, saboda ka fara sanin gaskiya sai ka san ma’abotanta, ka karanta tarihin da ke hannumu da wanda ke hannunsu ,   

وبشر عباد الذين يستمعون القول فيتبعون أحسنه

Kayi bushara ga bayina wadanda suke sauraron Magana su bi mafi kyawunta.

Allah shi ke shiryarwa ya zuwa daidai da gaskiya lalle shine mafi alherin mai taimako dukkanin godiya t tattabata ga ubangijin talikai.

 

Tarihi: [2017/4/11]     Ziyara: [678]

Tura tambaya