mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tambayoyin da akafi karantawa

Yaya zan kubuta daga ciwon fusata kan `ya`yana

sadar daku da lafiya da dukkanin iyalai masu karamci da muminai. Ya sayyid in saurayine mai aure ina kuma da yara biyu dayansu ya kai shekaru shida dayan kuma uku, sannan ina tsananin sonsu sai dai cewa matsalata shine ni ina yawaita daga murya da tsawa kansu ina kuma da saurin fusata koda kuwa abinda na fusata kai bai cancanci ayi fushi kansa ba kai wani lokuta tana kaiwa da in dokesu in musu tsawa, sai kuma daga baya iny nadama kan tsanantawa da kausasawata tareda su kai hatta tareda mahaifiyarsu a mafi yawa yawan lokuta, ina tambayar kaina me yasa na kasance haka ina mu’amala da su da fushi da matsawa tareda cewa ina tsanani sonsu, ya sayyid hakika ni a yarintata na fuskanci kausasawa daga mahaifina da mahaifiyata da `yan’uwana tun tun tasowata nake fuskantar kausasawa da matsaloli a gaban idaona naga yadda babana ke dukan mahaifiyata sannan muma bamu tsira ba yana dukanmu da tsananta mana da kausasa mana da zaginmu da korarmu kai da matsaloli da yawa yawn gaskiya da suka mai dani mutum mai kaushin dabi’a , tayiwu ragowar `yan’uwan suma haka suke, lallai mun ksance bama son mahaifinmu muna kanana yayainda muka girma mun nesanta daga gareshi kai har ta kai da bama zama waje daya tareda shi a mafi yawa-yawan lokuta sakamokon kaushin dabi’a da tsanantawarsa tareda mu, ni ban nufin sanya babana ya zama sababi cikin mu’amalata tareda iyalina sai dai cewa tabbas yana da wata rawa da ya taka cikin yadda na kasance ina mu’amala da iyalina.
ni ban nufin `ya`yana su fuskanci irin wahala da matsalolin dana fuskanta ni bazan haramtta musu ba kamar yadda babana ya haramta mini har aka wayi gari alakarmu a dangince ta raunana matuka, saboda ya sayyid na aiko maka da wannan wasika tawa ina mai fata lka taimaka mini da yadda zan fiata daga cutar fusata kan `ya`yana domin in samu damar yi musu mu’amala da tausasawa da jin tausayi da kalmomi masu kyawu wadda wadanda zasu kiyaye musu kimarsu da mutuncinsu da zatinsu nima kuma su kiyaye mini matsayina a wajen `ya`yana.
Allah ya saka muku da dukkanin alheri daga garemu kuma kada ya haramta mana albarkarku.

da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

Da zaka san cewa dukan da kake musu bai kasance don ladabtarwa ba kuma ya zarta haddin da shari’a ta iyakance, lallai lamarin yadda yake da zaka dokesu fatar wajen daka doka tayi jajawur toda sai ka biya diyya kuma wajibinka ka mikawa wanda ka doka daga cikin `ya`yanka bayan balagarsa ko kuma dai ka nemi ya yafe maka, idan diyya ta kasance mas’alar shari’a cikin duka kamar yadda cikin riosalolin fikihu  daga wajabcin diyya idan wurin da aka doka ya yi jajawur ko kuma yayi baki ko karyewa diyya ta kan sassabawa daga dinare miskalin zinariya ya zuwa dinare goma kerarra wadda ya kasance a zamanin imamai tsarkaka (as) ya sihe ka da ka dokesu da ace zakaji tsoron Allah da ranar kiyama ranar da iayaye ke gujewa dansu saboda tsananin hisabida binsa dalla-dalla, sannan abinda yafi kamata yayainda ka fusata ka danne fushinka ka zama mai hakuri da dauriya, idan baka tarbiyantar da kanka ba kan hakan to kai ka doki kanka mana me yasa zaka doki yaranka da matarka, idan kana cikin fushi zaka rasa hankalinka me yasa zaka doki yaraka doki kanka mana ka dauki takalmi a gaban yaranka ka doki kanka da karfi, lallai hakan zaifi tasiri kan yaranka fiye da ace ka dokesu, idan baka gasgatani ba ka jarraba aikata hakan kon da karo guda ne ka jarraba, ka bani labarin sakamako mai kyau da hakan ya haifar ko kishiyarsa.

Sannan idan babanka yayi maka mu’amala da kausasawa  to ai abinda ya dace shine ya zamar maka darasi aki sai ka yiwa yaranka da iyalinka mu’amala da tausasawa , saboda ai kai sakamakon kausasamaka kaji kana kinsa tun kana yaro karami ka ma guje shi byan ka girma, toh fa ka sani bata sauya zani ba haka lamarin dangane da kai da `ya`yanka, da zaki musu mu’amala da kausasawa da duka babu shakka tabbas baka gamsu da abinda babanka ya aikata maka ba, wani mawaki yana cewa : (kada kai hani kan wata dabi’a alhalin kaima kana aikata irinta lallai abin kunyane gareka idan ka aikata babban alaifi)

Sannan ciwaon fusata daga gareka yake maganinma na cikinka ai kaine kake fusata abinda yafi kamata ai kaine wanda zaka danne fushin kayi hakuri. Wajibi ka samar da wata kakkarfar irda da shauki  da soyayya mai ninkawa domin tarbiyantar da kanka da barin munanan dabi’u m,isalin fusata da kuma ka adontu da kyawawan halaye masu daraja kamar dauriya da hakuri lallai babu ko kokwanto zaka iya aikata hakan, saboda ta kaka za ace ka iya daga hannu ka doke yaranka da matarka abar tausayi fursuna gabanka amma baka iya dukan kanka ba ? ta kaka zaka fusata kan yaranka amma ka gaza fusata da kanka mai ywan umarni da munana, lallai ita tafi kusanci gareka daga matarka da yaranka me yasa ba zaka doketa ba kayi fushi da ita ba ka tarbiyantar da ita, me ya sameku ne kaka kuke hukunci, wannan wanne irin son kaine abar kyama ta kaka ni bana sonta a kaina amma kuma zan tarbiyantar da yarana da matata da ita.

Daga karshe ka komawa abinda na rubuta kan fushi da hakuri lallai an buga littafin an kuma sanya shi a sayit din alawy.net

Allah ne abin neman taimako.

 

Tarihi: [2017/5/27]     Ziyara: [472]

Tura tambaya