mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

: gameda hakkokin shari'a da ya ratayu kan miji da mata ai mana Karin


TAQATACCIYAR AMSA: dawwamar rayuwar aure da qarfafarta ya dogara da soyayya da qauna da fuskantar juna da girmama juna, addini muslunci domin iyali su samu tsayuwa da dawwama ya sanya haqqoqi ga kowanne xayansu ya kuma ayyana wasu wajibai kansu, duk sa'ilin da aka ce akwai haqqoqi to ubangiji na sanya wasu hukunce hukunce ciki, wannan maqala tana da danganta ka da tambayar da ta gabata kan haqqoqin maza da su ka hau kan mata, daga mafi girman haqqoqin maza na shari'a da na dokoki da suke kan mata.
1 dole mace ta rungumi shugabancin miji: idan cikin rayuwar auratayya wata matsala ta bijiro, to warware wannan matsalar na wajen miji sai da cewa wannan shugabanci na miji bai kamata ya fita daga kyawunta zamantakewa ba, ka da kasantuwarsa na haqqoqin shari'a da dokoki ya zamanto dalili da zai sanya miji munantawa iyali.
2 tilas mace ta mallakawa mijinta kanta: wajibi mata ta kasance cikin shirin amsa kiran mijinta don biya masa buqatarsa ta sha'awa sai dai idan ta na da wani uzuri na shari'a ko na doka da zai hana ta amsa kiransa kamar jinin haila da ke bijiro mata wata wata ko kuma wata rashin lafiya.
3 biyayyar miji a mahallinsu da gidan da suke zaune, sai dai idan mijin ya sallamawa matarsa wannan haqqi nasa, ko kuma a al'adarsu mace ke da wannan haqqi ku kuma wata larura mace ke da ita wadda za ta iya cutar da rai ko lafiyarta.
4 biyayyar miji a wajen gida da shigar da baqi cikin gida, a al'adance sai dai a lokacin sauke haqqin addini na wajibi kamar fita zuwa aikin hajji ko kuma fita don yin magani ko kuma ya zamanto zaman gida zai cutar da rai ko jiki da mutuncinta.
5 biyayyar miji da neman izininsa kan yin aiki a wajen gida da nau'in aiki, a yanayin da ya savawa al'adar zamanin da matsayin jinsin maza da mata ya kasance.

 AMSA FILLA FILLA: Allah maxaukaki ya halicci mace da namiji da yanayin da kowanne xayansu na buqatuwa da xaya buqatuwar  gangar jiki da ta ruhi, samuwa da wanzuwar kowanne ba ta yiwuwa ba tare da xayan ba, kammaluwar ruhi da gangar jiki ba ta yiwuwa sai suna tare da juna, masana hikima na cewa kowacce halitta yanki ne daga wata halitta kamamalalliya, dukkaninsu tawayayyu ne matuqar basu kasance tare da juna ba saboda kowanne xayansu na kammala xaya.

Bisa lura da banbanci tsarin  halittar jikin mace da namiji da banbancin ruhi sai ubangiji ya sanyawa kowanne xayansu hukunce hukunce da haqqoqi da sukayi tarayya cikin wasunsu, a wasunsu kuma kowanne ya kevantu da nasa don samun lamincin buqatun duniya da na lahira  ga kowanne xayansu.

Waxannan haqqoqi da hukunce hukunce  malamai  sun kallesu daga mahanga uku: 1 mahangar fiqihu 2 mahangar kyautata xabi'a{akhlaq} 3 mahangar haqqoqi.

Sakamakon a wannan wajen muna yunqurin amsa tambaya da akayi kan haqqoqin mace da ke kan miji, sakamakon wajibai na akhlaq da ruhi suke kammala da cika wajiban haqqi da dokoki da kuma kasantuwar wajibai na fiqihu ba su da banbanci mai yawa da wajibai na haqqoqi da dokoki to zamu taqaita bayani kansu.

 wajibai da ayyuka na akhlaq:

ayyuka da wajibai na akhlaq da ke kan mace sun kasu kashi biyu kamar yadda ya zo a harshen riwayoyi sune qima da muhimmancin  zama da miji da tattala shi.

  Manzon Allah{s.a.w} ya ce: da ace sujjada na halasta ga wanin Allah da na umarci mace ta yiwa mijintaا 

 

Haqqin miji kan matarsa yafi kowanne haqqi yawa da daraja

Jahadin mace shine jurewa cutarwar da mijinta ke mata.

 

Bai kamata mace ta fusa ta mijinta ba koda kuwa mijin ya cuta mata.

 

Ba a karvar aikin dukkanin matar da mijinta ke fushi da ita.

 

 Dukkanin matar da ba ta godiya ga mijinta dukkanin aikin da ta yi ba za ta samu lada ba.

 

2 ayukan akhlaq na zama da miji:

Bai kamata ace mace ta na da karkata da sha'awar kallon wani wanda ba mijita ba idan ta kasa kiyaye hakan to matsayin  mazinaciya ta ke wajen ubangiji.

 

Tilas ne mace ta kasance ta na amsa buqatun sha'awa na mijita a kowanne lokaci da kowanne yanayi ko da kuwa ta na kan gadon bayan raqumi dole ne idan ya nemeta ta amsa buqatarsa, idan kuma ta qi aikata hakan to  mala'iku za su la'ance ta.

 

Bai halasta mace ta yi azumin mustahabbi ba tare da izinin mijinta ba, da dukkanin aikin mustahabbi.

 

Bai kamata mace ta tsawaita sallah ba ta yanda yin hakan zai hana amsa buqatar mijinta.

 

Bai kamata mace ta yi sadaqa ba tare da neman izinin mijinta ba.

 

Bai halasta mace ta fita wajen gida ba tare da izinin mijinta ba, idan ta aikata hakan mala'ikun sama da qasa zasu yi ta tsine mata har lokacin da za ta dawo gida.

 

Ya kamata mace ta cancaxawa mijinta ado ta sanya turare, bai halasta ta sanyawa wanda ba mijinta ba turare idan ta qi kiyaye hakan sallolinta ba za su karvu ba.

 

Wajibai na haqqoqi da doka:  za mu yi bayanin haqqoqi da mace da miji su kayi tarraya da wanda ba suyi tarayya ba ciki.

Wajibai da mata da miji su kayi tarayya ciki:

 

1 Kyautata zamantakewa da juna: wajibi ne mata da miji su kyawunta zamantakewar su ta rayuwar aure dole ya zamnato akwai tausasa harshe da sakin fuska da murmushi tsakanin junansu  kamar yadda yake wajibi su qauracewa munanawa juna da miyagun kalamai sai idan yin hakan na da wani uzuri na shari'a ko na al'ada.

 

2  taimakon juna: dole ne mata da miji ya kasance suna aiki kafaxa da kafaxa don qarfafar  rayuwar su ta iyali da cigabanta, ma'aunin wannan  taimakekeniyar juna ya xoru bisa al'adun inda suke rayuwa, kamar misali ace  idan a al'adun wajen da suke rayuwa  ya zamanto shayarwa da lura da gida  na wuyan mace sannan ayyukan wajen gida na kan wuyan miji to a irin wannan lokacin ya kamata matar da mijin su haxu su taimakawa junansu don sauke waxannan ayyuka.

 

3 tarbiyantar yaro: mata da miji ababen tambaya tambaya ne kan tarbiyyar xansu gwargwadon ikonsu bisa  la'akari da wajen da suke rayuwa da zamani da al'ada, dole ne su zage dantse su yi iya qoqarinsu wajen yi masa tarbiyyar ta gari.

 

4 cika alqawari: bai halasta mata da miji su qulla wata alaqa wadda ta savawa shari'a da wani mutum daban.

 

Wajibai da suka kevantu da mace:

1 rungumar shugabancin miji: idan ya kasance wata matsala ta bijiro musu cikin rayuwarsu ta aure to warware wannan matsala na hannun miji sai dai cewa bai kamata miji ya fita daga da'irar kyautata zamantakewa ba yayin da yake yunqurin warware wannann matsala ka da kasantuwar shari'a da doka ta bashi dama ya zamanto dalilinsa na yin amfani da wannan damar ta hanyar da ba ta dace ba.

 

2 salllama kanta ga mijinta: ya kamata mace ta kasance cikin shiri amsa kiran buqatuwar mijinta ta sha'awa gwargwadon iyawar jiki da ruhi bisa al'ada sai idan ta na wani uzuri na shari'a ko al'ada kamar misalin jinin haila ko rashin lafiya wanda zai hana ta hakan.

 

3 biyayya ga miji a cikin gida, sai dai idan shi mijin ya sallama wannan haqqi na sa ga matar tasa, ko kuma ya kasance savanin al'adar  zamantakewa da aka saba da shi ya zamo ace biyayyar na hannun mace ko kuma  ya kasance akwai larura da za ta iya cutar da rai ko lafiyar  ita macen.

 

4 biyayyar miji a wajen gida cikin fitar ta unguwa da shigowar baqi cikin gidan, sai cikin sauke haqqin shar'a na wajibi ko neman magani a irin wannan wuraren wannan wajibi na saraya, ko kuma idan zamanta cikin gida na iya cutar da lafiyar ta da mtuncinta.

 

5 biyayya da neman izinin miji cikin yin aikin kwadago da irin nau'in aikin cikin yanayi da ya savawa al'adar zamani da wajen da suke rayuwa da jinsin mace da na miji.

Ya zuwa yanzu munyi bayanin haqqoqin miji kan matarsa ataqaice, yanzu za muyi qoqari yain bayanin haqqoqi mace kan miji ataqaice.

Kasha na uku haqqoqin mace da ke kan miji: haqqoqin mace da ke kan miji sun kasu kasha biyu 1 haqqoqin kyautata xabi'a{akhlaq} 2 haqqoqinta na shari'a.

Haqqoqin kyawunta xabi'a a mahangar riwayoyi;

1 kyawunta halayya tare da mace: ya zo cikin hadisi cewa son mata na daga xabi'un  annabawa{as}.[1]

2 nuna soyaya da qauna ga mata annabawa ba sa gafala da shi cikin kowanne hali.

3 kau da kai da yafiya ga mata yayin da suka nuna wata halayya mara kyawu.

4 murmushi da sakin fuska da kyautata musu mu'amala.

6 mafi kasantuwa abin so cikin maza shi ne wanda ya fi kowa kyautatawa ga matarsa.

7 jin tsoron ubangiji da qauracewa take haqqin matarsa.

 

Wajiabi na akhlaq:

1 dole ne ya dinga kallon matarsa kamar matsayin wata furen fulawa mai daxin qamshi ba wai ya dinga yi mata kallon baiwarsa ba.

2 dole ne ya tanadar mata kayyakin ado na zamani da kayan sawa  da kayayyakin marmari musammam lokutan bikin  sallah

3 ya kamata ya dinga shawara da matarsa cikin muhimman lamuran rayuwa.

4 kiyaye haqqoqin da akhlaq na kusantar mata don biyan buqata.

 

Haqoqi da suka kevantu da miji.

1 bada kuxaxe ga matarsa  don sauke haqqin ciyarwa.

                2 samar mata da abin da za ta ci gwargwadon yadda bai savawa al'ada ba da inda suke rayuwa ba.

3 samar mata da tufafin da za ta sanya gwargwadon al'adar garin da suke rayuwa.

4 samar mata da gidan da zata zauna bisa yadda al'adar inda suke rayuwa.

5 samar mata kayayyakin ado daidai gawragwado.

6 samar mata da mai mata aikace aikacen gida idan haka al'adunsu suka tafi kai ko kuma saboda larura ta rashin lafiya.

7 samar mata da magani yayin rashin lafiya.

 

Haqqoqin kusantar juna don biyan buqatuwar sha'awa:

Dokoki sun kame baki a wannan fage sun wadatu da kyautata zamantakewa, sai dai cewa malaman fiqihu sun kasa abin zuwa kashi biyu.

1 haqqin mace da ke kan mijinta  shi ne cewa idan miji ya auri budurwa to dole ya shiga xakinta har zuwa tsawon kwanaki bakwai idan kuma bazawara ce to kwanaki uku, idan kuma matarsa xaya to dole cikin kwanaki huxu ya bata dare xaya ragowar ukun kuma ya na da yanci yin yadda ya ga dama da su, idan kuma ya na da mata da yawa to cikin huxu kowacce na da xaya.

2 kusantar jinsi ta biyan buqatar sha'awa: wajibi ne  miji ya kusanci matarsa sau xaya cikin watanni huxu kasantuwar h


[1] Urwatul wusqa kitabul nikah sh 626

Tarihi: [2017/5/29]     Ziyara: [706]

Tura tambaya