mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Ta yaya zan samu malamin tarbiya cikin suluki da tarbiyyar irfani

Salamu alaikum
Ina yawan karance karance game da irfani ya bayyana cewa lallai ya zama larura gareni in fara suluki kan tsare-tsare sannu-sannu, tare da cewa ni na amfanu sosai, shin zaku iya taimaka mini don in fara ta hanyar wani malami ko da kuwa ta hanyar aiko da sako na yanar gizo (email) musammam da yake ni ina zaune kasar kanada (Canada)

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Tabbas irfanin muslunci na gaskiya shi ne wanda ya samu goyon baya da karfafa kuma halascinsa da asalinsa suka ginu kan kur’ani da ahlil-baiti tsarkaka  muhammad da iyalansa tsarkaka amincin Allah ya kara tabbata garesu ba wai abin da wadancananka ke da’awa ba ingantaccen irfani shi ne wanda ya zo daga ahlil-baiti shi ne tatacce, sannan duk da cewa a karshen karshen zamani sun sawa irfani sunan irfanin nazri da da amali sai dai cewa jigo shi ne aiki da bayanin daga hukunce hukuncen shari’a  tsarkakka na farkonta shi ne watsi da aikata ayyukan haramun da sauke wajibai, saboda kayi bakin kokarinka cikin kasantuwar abin da ka tsara na ibada shi ne aiki da abin da ya zo cikin risala amaliyya (littafin hukunce-hukunce) ga marji’in da kakewa taklidi cikin hukunce-hukuncen shari’a  cikin hanyar tarbiya kuma ka lazimci kur’ani  da mafatihul jinan wannan shi ne abin da zai kaika ga abin da ya zaka tuke gareshi da izinin Allah cikin lokacinsa   

وقال رسول الله صلى الله عليه وآله وسلم: (أدبني ربي فأحسن تأديبي)

Manzon Allah (s.aw) ya ce: ubangijna ya yi mini tarbiyya sai ya kyawunta tarbiyyata.

Duk wanda bai da malami tabbas Allah ne malaminsa  mai koyar da shi da ladabtar da shi da sannu zai turo maka wanda zuciyarka zata nutsu zuwa gareshi cikin suluki da tafiya (sairi) inhsa Allah kada ka debe tsammani daga rahamar Allah da tausayinsa da ludufinsa mai girma boyayyu

Allah ne abin neman taimako

 

Tarihi: [2017/11/7]     Ziyara: [384]

Tura tambaya