mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Naso neman Karin bayani daga gareka kan azkar wanda kayi ishararsu cikin littafin ulumul garbiyya

Salamu alaikum
Ina rokon Allah madaukaki mai girma da ya kara maka ilimi da haske alfarmar habibul Mustafa (s.a.w) sayyid ina kaunar neman Karin bayani da tambayarka gameda azkar wadanda kayi bayaninsu da ishararsu cikin littafin ulumul garbiyya misali duk wanda ya karanta ya muhaiminu kafa 125 lallai badininsa zai tsaftata zai kuma tsinkayi hakikanin abubuwa, shin wannan zikiri za a karantashi gwargwadon 125 sau daya a rana ko kuma duk duk sanda yinin ya mika sai a karanta 125 asuba 125 azuhur 125 magariba 125 sai natija tafi sauri.
Tambaya ta biyu: wadannan wuridai har zuwa wacce rana mutum zai fara tsinkayar tasirinsu misalign tsaftatar zuciya da waninsa?
Tambaya ta uku wacce it ace ta karshe sayyid ina son da zakai mini karamci da wani wuridi ayyananne da za mu rungume shi yau da gobe zan kasance maim aka godiya sayyid mai girma?

sunan Allah mai rahama mai jin kai

1-daga cikin sanannun azkaru  da auradu tabbas ayyananne adadi na daga cikin sirrinsa lallai shi yana matsayin sunnoni makulli duk anda ya yi kari ko ya tauye ba zai bude kofa b, shaik baha’i ya buga misali cikin littafinsa mai suna kashkul duk wanda ka ce masa mita `dari zaka kai ga taska lallai shi da zai kai ga mita 99 ba zai kai ga wannan taska ba haka ma da zai taka mita 101 nan ma ba zai tsinkayi wannan taska ba, saboda haka shi adadi yana taka rawa cikin zikiri Allah ne mafi sani.

2-tasiri yana biye da iklasi kamar yadda ya zo cikin riwaya :

 (أخلص تنل)

ka tsarkake niyya za ka samu

lallai daga cikin masu iklasi akwai wanda yake ganin tasirinsa tun daga farkon faraway cikinsu kuma akwai wanda bai iya gani sai bayan shekaru.

3-daga cikin abubuwan da ni a kankin kaina na jarraba su suka bani taufiki da alheri na zahiri da na badini shine zikirin ya wahhabu sau 14 na kanyi daya a sujudul shukri bayan kowacce salla, mustahabbi ne mustahabbi mai karfi cikin kowacce salla yin sujjadar godiya da godewa Allah sau 100 ya dinga fadin shukran ko kuma yace shukru lillah kafa uku  sannan bayan hakan sai ya ambaci ya wahhabu kafa 14 Allah ne mai datarwa.   

 

Tarihi: [2017/11/8]     Ziyara: [3446]

Tura tambaya