mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Taambayoyin karshe

Wasu daga cikin tambayoyi

Ina da tsoro mai tsananin gaske da cewa kada ya kai ga mata ta ta haramtu daga gare ni har abada saboda yawan furta Kalmar na sake ki kan harshe na da nake ko da yaushe.


Sayyid ni na jarrabtu ban sani ba ciwo ne ko kuma wani al’amari ne waki’i,
na gano cewa wankan janaba ta ya kasance bisa kuskure nayi shi sai daicewa gabanin gano hakan na kasance na dauki damarar tafiya umara sai na tambayi daya daga shehunan malamai sai yace mini wajibi ka koma makka mai karamci to shine tun wannan lokaci sai na ksance cikin kokwanto shin umarata ta inganta ko kuma gurbatacciya ce sai dai cewa bayan shudewar lokaci na kara tuntubi wani shehi yaje mini umara da niyyar na’ibantaka amma duk da haka ina cikin matsanancin tsoro da razani kan kada ya kasance mata ta haramta gareni har abada
daya nukdar shi ne tsahon lokaci Kalmar na sake ki ta wayi gari tana fadawa kan harshen kowanne lokaci tare da cewa ni cikin igiyar aure kuma ban sadu da mata ta ba tsahon shekara saboda ina tsoran cewa ta haramtu gare ni har abada sakamakon furta Kalmar saki da nake yi, ni yanzu ban san me ma zanyi ba?
Rayuwa ta da mata ta zata rushe idan na cigaba kan wannan hanya.
Daga karshe ina sauraron nusantarwarku ina kuma fatan ku bani wani zikiri ko wuridi da zai karfafa ruhina

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Tun farko abin da ya kamace ka shi ne kada ka je wajen wani shehi kamata ka rubuta tambayarka zuwa ga marja’in da kakewa taklidi ka nema amsar tambayarka daga gare shi da kuma neman ya bayyana maka abin da ya wajabta kanka ka aikata, kamar yadda Abu mislu ke cewa ka wurga tambayar wuyan malami kai ka fita daga cikin lafiya lau ko kuma babu wani taklifi kanka  cikin zmanin gaiba kubra  fiye da ka tuntubi marja’inka, sannan duk abina ba wannan bal allai yana daga wasawasin shaidani domin takurawa muminai saboda haka ka gaggauta yin watsi da wannan aiki na furta kalmar saki ka je ka morai rayuwarka tare da matarka bayan ka san hukuncinka daga marja’in da kakewa taklidi. Allah ne abin neman taimako.

 

Tarihi: [2017/12/19]     Ziyara: [716]

Tura tambaya