mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Shin yin saki cikin halin fushi ya inganta, sannan kuma cikin auren mutu’a akwai saki?

Na yi auren mutu’a wata mata daga matan da ba kabila take ba.. sai dai cewa bayan wani lokaci wannan mace da na aure ta hi’ince ni ta hanya alaka da wani mutum daban sai cikin fushi na gaya mata cewa auren ya mutu na sake ki, sai dai cewa kuma da baya tayi nadama mai tsanani ta kuma tuba ta furta Kalmar shahada ta zama musulma tana yin sallah musluncinta ya kyawunta, sannan ta nemi in cigaba da mu’amala da ita a matsayin mata ta, sai kara maimaita karanta sigar auren mutu’a sannan ta karba ta yarda sai dai cewa hakan ya gudana ba tare da sanya lokaci iyakantacce ba.
Wannan baiwar Allah tana da tsanani bukatuwa da in kasance tare da ita sakamakon muna aiki tare da juna a wuri guda da babu kowa sai ni da ita sannan mun larurantu mu kasance tare da juna tsahon awanni goma a wajen aiki… lallai ta koyi sallah daga wurina da lazimtuwa da addini sannan tana bukatuwa da kara koyo fiye da haka game da muslunci..
Wannan baiwar Allah bayan musluntarta dabi’unta da sulukinta sun sauya matukar sauyawa ta wayi gari tana kara samun nutsuwa tare da sannan lallai ita tana tsoron ka da in barta sai ya zama ta raunana ta kara bacewa hanya a karo na biyu… sai dai cewa matsalar shi ne:
shin zartar da sigar aure daga gare ta karo na biyu da nayi da rashin ayyana lokaci iyakantacce shin sakamakon hakan za ai la’akari da sigar matsayin gurbataciya?
Shin gaya mata da cewa na sake ki bayan gano ta da nayi a baya sakamakon alfasha da ta aikata tare da wannan mutumin ba a laka’ari da shi matsayin saki sakamakon ya faru sakamakon fusata da nayi.
Lallai ni ina tsananin bukatar amsa cikin gaggawa sakamakon tsananta matsaya.
Amincin Allah ya tabbata gare ku

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Da farko dai auren mutu’a babu saki cikinsa sai dai cewa in anso rabuwa da juna zai iya gaya mata kalmar :

 

 ( وهبت لك المدّة أو وهبت لها المدّة )

Na yafe miki kwanaki, idan kuma bata halarci inda yake ba zai iya cewa: na yafe mata kwanakin.

Na biyu: saki kadia yana cikin auren dindin, ya kuma tilas cikinsa a samu haduwar sharudda daga cikinsu halartar mutum adali da zai ji sigar sigar sakin tsuran fadin ke sakakkiya ce bai kasancewa saki a kankin kansa.

Na uku: me kake nufi da ha’inci idan ya kasance tsuran tattaunawa ne ko kuma wasa da juna ba tare da saduwar jinsi ba to hukuncinsa daban yake.

Na hudu: idan matar ta kasance wacce mutumin ya taka da sannan ya nufi ya aureta auren dindin ko kuma auren mutu’a to babu bukatar ya yin idda, domin ita idda ana yinta idan wani mutumin daban ya nufi auren ta ba shi ba.

Na biyar: rikonta da muslunci au ne mai kyawu matuka zaku ta samu lada kan hakan da izinin Allah.

Na shida : kamar yadda muka ambata babu idda ga aurawar kansa idan ya nufi ya maimaita kulla siga da ita sai dai cewa kawai daga auren farko zai jira zuwa karewa kwanakin da ya diba, kamar misali ya kulla aure kansa na shekara guda  sai shekarar ta kare  sannan ya kulla wani karo na biyu, idan ya nufi kulla sigar aure kanta gabanin karewar ta farko lallai sai ya yafe mata abinda yayi ragowa daga kwanaki  a matsayin saki sannan ya sake kulla sigar sabuwa, in ba haka ba aure kan aure bai halasta a shari’a.

Na bakwai : kamar yadda muka ambata babu saki cikin auren mutu’a asalan kadai dai akwai damar rabuwa sannan rabuwar na kasantuwa ta hanyar yafe mata kwanakin da aka ayyana da sukai ragowa.

Ina rokar muku Allah ya datar daku, kayi kokarin sanin wazifarka ta addini gabanin fara kowanne aiki sai ka zama cikin farin ciki duniya da lahira. Allah ya dawwamar daku cikin alheri da lafiya  
Tarihi: [2017/12/20]     Ziyara: [600]

Tura tambaya