mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Tambayoyin da akafi karantawa

Ta yaya zan samu kusanci zuwa ga Allah tare da cewa ina da bashin sallolin da ibada wuyana ban sauke su ba?


Salamu Alaikum
Shin ya halasta mutum ya nemi kusanci da Allah mai girma da daukaka tare da cewa a wuyansa akwai bashin sallolin da suka wuce shi bai yi su ba?

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Neman kusanci zuwa ga Allah wajibi cikin kowanne hali da yanayi cikin kowanne lokaci da bigire, lallai ita kofar Allah a bude take siradi zuwa gare shi mike yake ga wanda ya kasance daga cikin masu zunubai sai ya tuba ya koma ga Allah. Haka ma ga wanda ya kasance daga salihai, kowa da kowa tare da annabawa da siddikai da shahidai da bayin Allah nagargaru cikin siradi mikakke wanda Allah ya yi ni’ima da shi kansu madalla da wannan aboki, idan ya kasance ka tabbatu zuwa ga Allah sai ka kasance daga tare da wadancan cikin siradinsu mikakke babu abin da ya rage gare ka face ka zage dantse ka sauke bashin sallolin da azumin da suka fauce maka ka kuma sauke hakkoki mutane da suke rataye wuyanka sannan ka da ka koma aikata zunuban da ka tuba daga aikata su domin tubanka ta kasance taubatan nasuha, tabbas Allah mai gafara mai jin kai ne mai suturce laifuka mafi jinkan masu jin kai, lallai shi ne mafi alherin masu taimakoda tallafawa karshen maganarm dukkanin godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai 

Tarihi: [2018/1/7]     Ziyara: [356]

Tura tambaya