mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wadanne ilimummuka ne mafi muhimmanci da za karanta su don kaiwa ga martabar ijtihadi? Shin ilimin dirayal kalam da falsafa da irfani da tafsiri sharaɗi ne cikin yin ijtihadi ?

daga cikin sanannen al’amari cikin ijtihadi a mazhabar shi’anci mai albarka shine cewa lallai ɗalibin ilimin addini har ya kai martabar ijtihadi wacce martaba ce da aka shardanta ta kan marja’in taklidi- ya zama dole ya kasance ya koyi wasu adadin ilimai misali kamar ilimin lugga manɗiƙ da ilimin rijal da usulul fiƙihu da fiƙihu.
Hakika munga wasu malamai suna sharɗanta koyan wasu iliman daban kamar kalam falsafa irfani kai har da ijitihadi cikin ilimin tafsiri.
Saboda haka mene ne ra’ayinku cikin sharɗanta waɗannan ilimai a matsayin shimfiɗa don kaiwa ga martabar ijtihadi da kuma kasantuwarsu sharaɗi ga wanda zai da’awar marja’iyya da yin fatawa ga mutane

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Istinbaɗin hukunci shari’a daga dalilansa na filla-filla bai da wata dangantaka da ilimin kalam da falsafa da irfani da ilimin tafsiri ta ƙaƙa waɗannan ilimai za su kasance shimfiɗa gareshi ballantana ma ace za ai istinbadi daga cikinsu.

bai buya ba cewa lallai mujtahidi faƙihi yana da kewaya da waɗannan ilimai a jumlace sai dai cewa kewaya da su wani abu ne daban kuma ijtihadi daga cikinsu wani abu ne shima daban 
Tarihi: [2018/2/5]     Ziyara: [556]

Tura tambaya