mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Ta kaka zan furta harafin ض a cikin sallah?


Salamu Alaikum sayyid
Inada wata matsala lallai duk yanda nakai da bakin kokarina wajen furta harafin ض cikin kalmar magdubi wad dalin. Ni ba san me yasa wasu ke cewa sallarka ta lalace akwai matsala cikin sallarka matukar baka furta wannan harafi daidai ba, ni na daina yin sallah sakamakon haka, ni yanzu ban san ya zanyi ba na gaji na gigice.
Ina fatan taimakonku da addu’arku gareni lallai Allah zai ji tausayi na da koyon yadda ake furta wannan harafi.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

Ina jan kunnenka ina jna kunnenka daga makiyinka iblis mai nacin kiyayya da rundunarsa daga aljannu da mutane, lallai shi ya rantse da Allah da buwayar Allah tun ranar farko da cewa tabbas sai ya halaka bil adama face bayin Allah tsarkakakku daga cikin makircin iblis shine wasiwasi da tasawwulat da yunkurin ya fitar da kai daga kan hanyar addini, dubi yadda a kan hanya kasantuwar kai baka iya furta harafin dadun daidai ya fitar da kai daga addini baki daya, saboda sallah itace jigo ginshikin addini duk wanda ya barta ya zama kafiri mai kafircewa ni’imar Allah kuma fasiki za kuma a tashe shi tare da fir’auna da hamana. Batun harafin dadun zahiri magana shi ne baki dayan fakihai maraji’ai sun bada fatawar cewa ka zo da abin da zaka iya daga furta shi, Allah bai dorawa rai face abin da a yalwace ta. Saboda sallolinka sun inganta yanzu abin da ya rage gare ka shi ne rama sallolin da ka bari bakai saboda zarginka na baka iya fadin harafin dadun ba, sanna ka himmatu da sallah lallai itace amudin addini kada ka sake ka kara barin sallah cikin kowanne hali

Ina hadaka da Allah ina hadaka da Allah cikin sallarka.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/2/20]     Ziyara: [387]

Tura tambaya