mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Matsalolin ma’aurata

Salama Alaikum
Hakika ni sharifiya ce ina kuma da aure sai mijina ya ga wasu hotunan soyayya cikin waya ta sai ya dauka cewa ni ina wasu abubuwa da basu dace ba yanzu haka ya kaurace mini yana kuma son sakina, ina neman taimakonku.

 

Salama Alaikum

Hakika ni sharifiya ce ina kuma da aure sai mijina ya ga wasu hotunan soyayya cikin waya ta sai ya dauka cewa ni ina wasu abubuwa da basu dace ba yanzu haka ya kaurace mini yana kuma son sakina, ina neman taimakonku.

 Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ki gaya masa cewa ke kina son sa kina son ya dinga nuna miki soyayya, lallai hakan abu ne mustahabbi ki gaya masa ina nuna maka soyayya ne domin cika kaunarka da kuma son in ga kai na cikin kariyarka da kulawarka domin ni mace ce rarrauna ina bukatuwa da majingina da amudi karfaffa da zan jingina jikinsa, lokacin da nake kankanuwar yarinya na jingina jikin babana yau kuma gani matar wani ina jingina da mijina, ashe ba maza sune masu tsayuwa kan sha’anin mataye ba? Sannan Kalmar (Kawwamun) da ta zo cikin kur’ani mai girma da siga ta mubalaga kan wanda suke tsayuwa da tsayawa ma’anarsa shine namiji ya tsayu kan dukkanin sha’anunnukan matarsa daga ciki akwai nuna soyayya gareta da kauna, da zaka bayyana mata soyayyarka gareta ko da ba ta kyautar flower ne yar karama cikin tunawa da zagayowar ranar aurenku ki ce masa lallai yau ni ba zan fita wajen aiki ba har sai ka kusanto ni ka nuna mini soyayya, ya zama dole gareka ya masoyina ya amudin haima ta ya fitila rayuwata ka riske ni ka fahimce ni ka yi bincike kan dalilin abin da na aikata bawai kayi tunanin kaurace mini ba da sakina lallai mafi kiyayyar halal wurin Allah shi ne saki saboda me ya sa ka yanke wannnan shawara alhalin mafi kyawun kalma ga diya mace kamar yadda Imam Sadik (a.s) ya fadi daga manzon Allah (s.a.w) shi ne mijinta ya ce mata (ina sonki) lallai lallai hakan ba zai bushe ba cikin zuciyarta bari dai za ta fansar da ranta ga mijinta, babu tsimi babu dabara sai da Allah madaukaki muna neman tsarinsa daga jahilci da wauta da rashin kyawunta tafiyarwa da rayuwa mani’imciya mai dadi da cike da farin ciki don kada mutum samaratakarsa ta tafi cikin hayaniya da jayayya da tunanin mai zai kasance gobe ga yayansa lallai tunani dan kankanin lokaci yafi alheri daga ibadar tsawon shekara kamar yanda ya zo cikin hadisi. Allah ne abin neman taimako    

Tarihi: [2018/4/23]     Ziyara: [331]

Tura tambaya