mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Wasu daga cikin tambayoyi

Ta yaya zan samu rabauta da kulawar Sahibuz-zaman

Ta yaya zan samu rabauta da kulawar Sahibuz-zaman (A.f) ta yaya zan kai zuwa gare shi? Shin akwai wani ayyanannen zikiri kan hakan?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Za ka samu kulawarsa ta hanyar yin tsarkakakkiyar biyayya ga Allah da tak'wa da tsantseni kamar yanda ya zo daga gare su amincin Allah ya kara tabbata a gare su, bawai ta hanyar yin wani ayyanannen zikiri tare da kin barin sabon Allah wa'ayazubillah, Allah ne abin neman taimako, farin ciki ga wanda yake tunanin ta yaya Imamin zamaninsa zai yarda da shi ta yaya zai isa zuwa gare shi, lallai Imam ya na son ya ga mun kiyaye tsoran Allah kamar yanda annabawan Allah da kakansa Mustafa suka so hakan daga garemu, farin ciki ga masu tak'wa cikin aljannoni da koramu wurin sarki mai ikon yi cikin lahirarsu da duniyarsu wurin Imamin zamaninsu amincin Allah ya kara tabbata a gare shi kuma Allah ya gaggauta bayyanarsa madaukakiya.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/4/27]     Ziyara: [349]

Tura tambaya