mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Ina da matsalar raunin motsin sha’awa shin ya halasta in karanta littafin kissoshin batsa?


Samahatu Ayatullah Sayyid Adil-Alawi Salamu Alaikum, ni ina da shekaru kimanin 28 kuma nayi aure sai dai cewa in fuskantar raunin sha’awa matuka, shin yana halasta gareni in karanta hikayoyin motsa sha’awa domin sha’awa ta ta samu motsawa?
Ka taimaka mini Allah yayi maka rahama sakamakon su wadannan hikayoyi basa dauke da hotunan batsa.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Dukkanin aikin da ya sabawa shari’a na motsa sha’awa bai halasta kamar misalin hikayoyin batsa ko kallon fima-fiman batsa ko wani abu makamancin haka ko da kuwa ya kasance share fage don yin jima’I da shari’a ta halasta domin cewa yanda lamarin yake shine ba a da’a ga Allah ta hanyar saba masa.

Tarihi: [2018/7/31]     Ziyara: [294]

Tura tambaya