mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

ina neman wani aiki daga hannun ma'aikatar harkokin cikin gida

ina da wata bukata ga ma’aikatar cikin gida

Salamu Alaikum samahatus sayyid Adil-Alawi (h)

Atakaicce ina son bayyana muku cewa na gabatar da bukatar bani yin wani aiki ga ma’aikatar harkokin cikin gida amma kusan tsawon shekara guda da watanni biyu Kenan har yanzu ba a bani ba, sai gashi cikin kankani lokaci masu iyayen gida sun gabatar da bukata irin tawa kuma sun samu, amma mu `ya`yan talakawa marasa gata bamu da kowa sai Allah da manzonsa da iyalansa tsarkaka sune kadai gatanmu kuma tsaninmu.

Ina da wata bukata ga ma’aikatar cikin gida

Sayyid yaya zan yi Kenan lallai ni nayi baki kokarina harma na gaji, yanzu ta wacce hanya zan samu biyan wannan bukata daga wurin Allah madaukaki, ina neman ka sanar da ni ko da sallar neman biyan bukata ce ko dai wani abu da zai saukake mini biyan wannan bukata wurin ubangiji, daga karshe ina barar addu’a daga kan biyan wannan bukata.

Danku Ammar

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai

Na’am madalla da dukkanin mai yarda da hukuncin Allah da kaddararsa, sau da yawa kukan so wani abu alhalin bazai amfana muku komai ba, ba zai kuma kasance sababin cetonku ba, sabod ahaka abinda ya fiye maka ka fawwala lamari ga Allah ka kuma dogara gareshi, ka cigaba da nema shi dama motsi daga gareka yake amma albarka ta hannun Allah.

Sannan ka rungumi yin addu’ar tawwasuli da imamai har tsahon kwanaki arba’in muna rokon Allah ya biya maka bukatarka.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2018/10/9]     Ziyara: [196]

Tura tambaya