mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Hakika gabanin nunar hankalina na aikata wani babban laifi sai dai cewa daga bayan na tuba amma tare da haka mutane suna kallona a wulakance, ka nusantar dani mafita

Salamu Alaikum, Allah ya gaggauta bayyanar hujjarsa.
Hakika ni mutum ne dana aikata babban zunubi amma lokacin banda nunar hankali ban san munin wannan laifi hatta cikin zamantakewata da jama’a da cikin dabi’u na lallai wannan zunubi ana kirga shi munanan laifuka ababen kyama, Allah ne shaida na aikata shi lokacin rashin cikakken hankali, muhimmi shine na yarda na aikata wannan laifi nayi ikirari da shi a gaban Allah matsarkaki sannan ina ikirari da shi a gabanku, bayan shudewar zamani na tuba taubatan nasuha, na kuma yi tsananin nadama kan abinda na aikata, wannan abu ya faru ne kafin shekaru 18, sannan na fuskanci Allah madaukaki da lafiyayyar zuciya ina kuma bakin kokari cikin gyaran kaina da badinina, na fara sabawa kaina sakafantuwa da sakafar muslunci budaddiya, sannan yanzu na fara jin dadi cikin ruhina, sai dai cewa Sayyid abind ayake damuna ko da yaushe shine cewa mutane suna yi mini kallon wulakanci hatta kai ga wasunsu suna fadin Maganganu marasa dani a bayan idona, wani lokacin idan sukai mini wannan kallo na wulakanci sai inji kamar zuciyata zata tsige daga cikin kirjina, wallahi Sayyid Allah ne shaida lallai na tuba, amma mutane basa tausaya mini suna mugun takura mini, ka shiryar dani zuwa mafita, wallahi hatta kai ga ina fatan mutuwa da hutawa, shin akwai wani aiki da zai taimaka mini fita daga wannan abu ko kuma wani wuridi ko wata ibada???
Sayyid alal hakika ina cikin bukatar taimakonku, yayinda da nake wannan rubutu ina jin kunci da kunar rai hawaye na yana kwarara kai kace ambaliyar teku.
Allah ya dawwamar da rayuwarku ta zama amfani ga muslunci da musulmai.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya kai wannan tubabben matashi ka sani bai halasta ba kayi ikirari da zunubinka gaban kowa face Allah madaukaki, wannan na nuni kan rahamarsa da ludufinsa da suturtawarsa girmansa ya girmama, mu musulmi ba kamar kiristoci muke ba da mutum zai yi ikirari da zunubinsa cikin coci gaban fasto, sannan idan Allah ya karbi tubanka kada ka damu da duk abinda mutane ke surutu da shi kanka, kayi hakuri ka jure ka yi fatan hakan ya kasance kaffara gareka daga zunubanka, sannan na uku ita kasar Allah yalwa gareta kayi kokarin samun wani garin da mutane basu sanka ba a can, lallai kai ka tuba kana kuma gyaran kanka da ayyukanka, lallai shi Allah kyakkyawa zai bayyanar da kyawunka garesu ya boye munanan ayyukanka kai bari yana daga cikin kyawawan sunayensa (ya wanda ya bayyanar da kyakkyawa ya boye mummuna)

Allah ne abin neman taimako.   


Tarihi: [2018/12/16]     Ziyara: [236]

Tura tambaya