mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Mene ne ma’anar fadin ku bi ashrarai da sannu-sannu da dabi’unsu

Salam Alaikum
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
جَامِلُوا الْأَشْرَارَ بِأَخْلَاقِهِمْ تَسْلَمُوا مِنْ غَوَائِلِهِمْ ، وَ بَايِنُوهُمْ بِأَعْمَالِكُمْ كَيْلَا تَكُونُوا مِنْهُمْ " .
Ku bi Ashararai sannu-sannu da dabi’unsu sai ku kubuta daga sharrinsu, ku kaurace musu da ayyukanku don gudun kada ku kasance daga cikinsu.
Wannan hadisi ya zo cikin littafin Biharul-Anwar.

Tambaya anan shine mene ne ma’anar wannan hadisi?

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 Abin da ake nufi da shine ku bi a sannu kada ta kai ga kun samu karo cikin munanan dabi’unsu, idan jahilai sun muku Magana ku ce musu salamu alaikum, sai mutum ya kubuta daga sharrinsu ko kuma muce musiba da bala’i, a zahirance ku bisu a sannu amma a badinance ku kaurace musu da ayyukanku, ma’ana kada ayyukanku su zamanto irinta, shi masharrani yana aikata alheri da sharri, shi ko mumini yana aikata alheri da ihsani, ita kowacce kwarya na yayyafi abinda yake cikinsa, kowanne tsuntsu kukan gidansa yake

Allah ya sa mu dace.

Tarihi: [2019/1/2]     Ziyara: [175]

Tura tambaya