mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Jinin da akai afuwa kansa


Salam Alaikum
Tambaya: malaman Fikihu sun ce: jini akan jiki da kaya idan yawansa kasa da fadin dirhami to anyi afuwa kansa.
Ina neman Karin bayani kan wannan mas’ala?
Da digon jini ya kasance kasa da dirhami sai ya fada cikin kofin ruwa sai nayi wanka da wannan ruwa sai jikina ya najastu sai ruwna da ya fallatsu baki dayan jikina, shin hukuncin zai zama daya Kenan tareda cewa jinin da ya cudanya da ruwa ya fallatsu jikina ya zarta girman dirhami.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hukunci yana kanka tsantsar jini ne bawanda ya cudanya da ruwa matukar dai girmansa bai kai dirhami ba to anyi afuwa kansa cikin sallah, idan jinin ne tsantsa ya yadu to lallai babu afuwa kansa cikin sallah, digo daya ba shine ma’auni ba ma’auni shine girmansa kada ya kai girman dirhami digo daya ne ko fiye da haka.  

Tarihi: [2019/1/2]     Ziyara: [158]

Tura tambaya