mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Shin kumusi yana halasta ga `yan shi’a cikin zamanin gaiba

Salamu Alaikum shin lokacin gaiba kubura kumusi yana halasta ga shi’a, kamar yanda riwaya dauke da sa hannun Imamul Hujja (af) ta zo da bayani sannan wasu suna ganin cewa kumusi ya halasta ne a zamanin Imam Ali (a.s) domin tsafatatar `ya`yan shi’a kuma ka da suci kason Imami Ma’asumi daga kumusin.
Muna neman gamsashshen bayani daga gareku.

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai.

 mas’alar tana komawa zuwa ga Mujtahidi wanda ya cika dukkanin sharuddan ijtihadi cikin mukamin istinbadin hukunci, matukar dai kai mukalladi ba Mujtahidi ba to dile ne ka koma zuwa ga wanda kake taklidi da shi, sannan ka yi fatali da ratsatstsen ra’ayi ka yi riko da abinda ya shahara tsakanin malamai.

Allah ne abin neman taimako.

Na’am idan ka kasance masanin fikihu to ka iya komawa ga dukkanin riwayoyin  cikin wannan babi, riwayoyin sun kasu zuwa kasha 9 cikinsu akwai karo da juna dole ne ayi majma’ail urfi ko tabarru’I tsakankanin riwayoyin a wannan lokaci zaka san yaya zaka ciro hukunci kayi fatawa kamar yanda sauran masana fikihu sukai fatawa kan wajbacin bada kumusi a zamanin gaiba kubura, bai inganta ga wand aba masanin fikihu ya dauki riwaya daya ko biyu sannan cikin jahilci ya fitar da fatawa ya kyale sauran gurguzun riwayoyin, dukkanin wanda yayi fatawa ba tareda ilimi to ya nemi masaukinsa a wuta, lallai a kiyaye ayi taka tsanstan cikin shiga abinda ba fagenka ba, yanzu zai yiwu a ce mu kutsa kai cikin fannin likitanci mu rubutawa mara lafiya magani cikin jahilci lallai!

Lallai hakan yana daga abind aya haramtu haka cikin fikihu. Dole ne ko dai ka kasance Mujtahidi ko mukalladi ko Muhtadi, kowanne daga cikinsu ya san taklifin da yake kansa.

Wurin Allah ake neman taimako. 

Tarihi: [2019/1/4]     Ziyara: [215]

Tura tambaya