mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Kalamanku haske ne


Zantukanku haske
«عن عبد الله بن الفضيل الهاشمي قال: قلت لأبي عبد الله (عليه السلام): يا ابن رسول الله كيف صار يوم عاشوراء يوم مصيبة وغمّ وحزن وبكاء، دون اليوم الذي قبض فيه رسول الله صلى الله عليه وآله، واليوم الذي ماتت فيه فاطمة، واليوم الذي قتل فيه أمير المؤمنين، واليوم الذي قتل فيه الحسن بالسّمّ؟ ...
فقال: إن يوم الحسين أعظم مصيبة من جميع سائر الأيام، وذلك أن أصحاب الكساء الذي كانوا أكرم الخلق على الله عز وجل كانوا خمسة ... فلمَّا قتل الحسين لم يكن بقي من أصحاب الكساء أحد للناس فيه بعده عزاً وسلوة، فكان ذهابه كذهاب جميعهم ...».

 

Zantukanku haske

«عن عبد الله بن الفضيل الهاشمي قال: قلت لأبي عبد الله (عليه السلام): يا ابن رسول الله كيف صار يوم عاشوراء يوم مصيبة وغمّ وحزن وبكاء، دون اليوم الذي قبض فيه رسول الله صلى الله عليه وآله، واليوم الذي ماتت فيه فاطمة، واليوم الذي قتل فيه أمير المؤمنين، واليوم الذي قتل فيه الحسن بالسّمّ؟ ...

فقال: إن يوم الحسين أعظم مصيبة من جميع سائر الأيام، وذلك أن أصحاب الكساء الذي كانوا أكرم الخلق على الله عز وجل كانوا خمسة ... فلمَّا قتل الحسين لم يكن بقي من أصحاب الكساء أحد للناس فيه بعده عزاً وسلوة، فكان ذهابه كذهاب جميعهم ...».

An karbo daga Abdullahi Ibn Fudailu Alhashimi yace: na cewa Abu Abdullah (a.s) ta yaya Ranar Ashura ta zamanto ranar musiba da bakinciki da kuka koma bayan ranar da wafatin manzon Allah (s.a.w) da ranar da Fatima ta mutu da ranar da aka kashe sarkin muminai da ranar da aka kashe Hassan da guba?

Sai yace:: ita ranar Husaini tafi girmamar musiba daga sauran dukkanin ranaku, hakan ya kasance saboda su mutanen cikin bargo wanda suka kasance mafi karamcin halittu wurin  Allah Azza wa Jalla sun kasance mutane guda biyar… yayinda aka kashe Husaini sai ya zamanto babu wani da ya rage cikinsu bayansa girma da yaye bakn ciki, tafiyarsa ta kasance daidai da tafiyar dukkaninsu…

1- Ranar Husaini rana ce ta bakinciki mafi girma:

«من كان يوم عاشوراء يوم مصيبته وحزنه وبكائه، يجعل الله عز وجل يوم القيامة يوم فرحه وسروره».

الإمام الرضا (عليه السلام)

Duk wanda ranar Ashura ta kasance ranar musibarsa da bakincikinsa da kukansa, Allah zai sanya masa ranar kiyama ranar murna da farinciki.

عن الإمام الرضا (عليه السلام) قال: كان أبي (عليه السلام) إذا دخل شهر المحرَّم لا يرى ضاحكاً، وكانت الكآبة تغلب عليه حتى تمضي عشرة أيام، فإذا كان يوم العاشر كان ذلك اليوم، يوم مصيبته وحزنه وبكائه ويقول: هو اليوم الذي قتل فيه الحسين (عليه السلام).

An karbo daga Imam Rida (a.s) yace: babana (a.s) ya kasance idan wata Muharram ya shigo ba a ganinsa yana dariya, bakinciki na galaba kansa har zuwa ranar goma ga wata, idan ranar goma ta shiga wannan rana ta kasance ran ace ta  musibarsa da bakincikinsa da kukansa yana cewa: wannan itace ranar da aka kashe Husaini (a.s)

2- falalar yin kuka kan Husaini (a.s).

«فعلى قتل الحسين (عليه السلام) فليبكِ الباكون، فإن البكاء عليه يحطّ الذنوب العظام».

الإمام الرضا (عليه السلام)

kan kisan Husaini (a.s) masu kuka su yi kuka, hakika kuka kansa yana ruguje manyan zunubai.

«يا ابن شبيب! إن كنت باكياً لشي‏ء فابكِ للحسين بن علي (عليهما السلام) فإنه ذبح كما يذبح الكبش وقتل معه من أهل بيته ثمانية عشر رجلًا ما لهم في الأرض شبيهون».

الإمام الرضا (عليه السلام)

Ya Ibn Shabibu idan ka kasance mai kuka kan wani abu to kayi kuka kan Husaini Ibn Ali (a.s) hakika an yanka shi kamar yanda ake yanka rago, na kashe mutane tamanin daga danginsa tare da shi wadanda babu misalinsu a doran kasa.

«كل عين يوم القيامة باكية، وكل عين يوم القيامة ساهرة إلَّا عين من اختّصه الله بكرامته، وبكى على ما يُنتهك من الحسين وآل محمّد (عليهم السلام)».

الإمام علي (عليه السلام)

Kowanne ido ranar kiyama yana kuka, kowanne ido ranar kiyama bashi babu bacci face idaniyar da Allah ya kebanceta da karamarsa, tayi kuka kan keta alfarmar da akayiwa Husaini da iyalan Muhammad (a.s)

«كان علي بن الحسين (عليهما السلام) يقول: أيّما مؤمن دمعت عيناه لقتل الحسين (عليه السلام) حتى تسيل على خدَّيه بوَّأه الله بها غرفاً يسكنها أحقاباً ...».

Aliyu Ibn Husaini (as) ya kasance yana cewa: duk wani mumini da idaniyarsa ta zubar da hawaye sabida kisan da aka yi wa Husaini (a.s) har ta kai ga hawayen ya zuba kan kuncinsa Allah zai bashi masaukan falo-falo da ita da zai zauna tsahon lokaci…

3- addu'ar Imam Sadik (a.s) ga maziyarta Husaini  da masu kuka kan musibarsa.

«اللهم يا من خصّنا بالكرامة ووعدنا بالشفاعة .. اغفر لي ولإخواني وزوَّار قبر أبي الحسين بن علي صلوات الله عليهما

Ya Allah ya wanda ya kebance mu da karama yayi mana alkawarin ceto.. ka yi gafara gareni da `yan'uwana maziyarta Husaini Ibn Ali amincin Allah ya kara tabbata a garesu.

اللهم ... فارحم تلك الوجوه التي غيَّرتها الشمس، وارحم تلك الخدود التي جرت دموعها رحمة لنا، وارحم تلك القلوب التي جزعت واحترقت لنا، وارحم الصرخة التي كانت لنا، اللهم إني استودعك تلك الأنفس والأبدان حتى ترويهم من الحوض يوم العطش».

Ya Allah ka yi rahama kan wadancan fuskoki da rana ta sauya su, ka jikan wadancan kuncaye wadanda da hawayensu ya kwarara saboda tausayinmu , ka jikan wadancan zukata da suka gigita suka konana saboda mu, ka jikan ihun da akai saboda mu, ya Allah ni ina baka ajiyar wadancan rayuka da jikkuna hark a kosar da su daga tafki ranar kishirwa.

4- rera waka kan Husaini (as):

«من أنشد في الحسين بيتاً من الشعر فبكى وأبكى عشرة فله ولهم الجنة ..».

الإمام الصادق (عليه السلام)

Duk wanda ya rera waka baiti guda daya yayi kuka ya sanya mutane goma kuka to lallai yana da aljanna suma suna da aljanna.

 


Tarihi: [2019/4/9]     Ziyara: [164]

Tura tambaya