mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Tambayoyin da akafi karantawa

Shin tsarkake niyya tana da wahala ga gamagarin mutane

Salam Alaikum. Sayyid mai girma cikin daya daga mudarorin da kuka yina dangane da tsarkake duk wanda ya tsarkake niyyar sa tsahon kwanaki arba’in ya zuwa bayanin ku kan cewa bai tsaya iya nan ba kai har wanda ya tsarkake niyyar sad an karamin lokaci, wannan lacca da kuka tayi mini tasiri ta kawo wasu tambayoyi cikin zuciyata ina tambaya shin gamagarin mutum ma kuwa irina zai iya tsarkake niyyar sa?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Martabobin iklasi suna sassabawa da sassabawa martabobin mutane, lallai su sinfi uku ne: gamagari da kebantattu da kebantattun kebantattu kamar yanda al’amarin yake cikin takawa, lallai akwai takawar gamagarin mutane shine sauke wajibai da kauracewa haramun, kebantacciyar takawa shine barin shubuhohi ballantana ma abin ya kai ga haramun, sai ta uku itace takawar kebantattun kebantattu wacce ta kunshi hatta barin  halal (wadda hausawa suke cewa ana barin halal don kunya) ballantana ya kai ga aikata shubuha, to haka al’amarin yake cikin iklasi, idan ya kasance wanda riya take kishiyantarsa kamar yanda ya zo cikin hadisi kan bayanin riya ita riya tana sadadawa kamar misalin yanda tururuwa take tafiya cikin duhun dare kan dutse da babu wani tsiro kansa, waye zai iya jin karar ta da sautin tafiyar ta, to haka riya take shiga cikin ayyukanmu da ibadar mu, shin tare da wannan bayani yaya zamu fassara tsarkake niyya ma’ana iklasi shin yana da sauki Kenan za mu ce ko kuma yafi tsananin wahala daga daukar dutse?! Babu tsimi babu dabara sai da karfin Allah madaukaki

Allah abin neman taimako.

Tarihi: [2019/5/2]     Ziyara: [41]

Tura tambaya