mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Azkaru domin haskakar zuciya

Akaramakallahu ya taimaka mana da azkaru da su haskaka zuciya

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya zo cikin ingantaccen hadisi cewa:

(كلمة لا إله إلّا الله حصني فمن دخل حصني أمن من عذابي)

Kalmar babu abin bautawa da gaskiya sai Allah shinge na ce  kuma duk wanda ya shiga shinge na ya aminta daga azaba ta.

Wannan shine boyayyen zikiri kuma shine mafi falala har sau saba’in daga bayyanannen zikiri, shi baki dayansa haske ne sai dai kuma shi zikiri cikin sa ana bukatar halarto da wanda ake Ambato ga mai Ambato, ya zama dole bawa mai zikiri ya ga cewa wanda yake Ambato shine Allah yana cikin hallararsa, baki dayan halittu na cikin hallararsa kada ya yi ganganci saba masa yayi bakin kokarin ganin yayi masa biyayya, ya kuma jin tsoran sa hakika tsoronsa a wannan lokaci zuciyarsa zata haskaka da hasken Allah hasken sama da kasa, da hasken kur’ani (mun saukar da haske tare da shi) da hasken ilimi, sannan shi ilimi bai cikin yawan karatu bari dai shi ilimi haske ne da Allah yake jefa shi cikin zuciyar wanda ya so, da hasken Imam amincin Allah ya kara tabbata a gareshi (sammai sun haskaka da hasken ubangijinsu) da hasken dukkanin hakse daga sunayensa kyawawa da madaukakan siffofin sa, (ya Allah ina rokonka don haskenka da mafi haskakarsa da dukkanin hasken ka mai tsananin haske)

Allah ne abin neman taimako
Tarihi: [2019/5/8]     Ziyara: [150]

Tura tambaya