mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Shin Mahadi yana dora hannun sa kan kawunan bayin Allah


Salam Alaikum
riwayar nan da ta kawo batun cewa Imam Mahadi (as) yana dora hannun sa kan mutane shin tana nufin hankulan mutane zasu samu kammaluwa da kuma barin aikata sabo, ko kuma dai babu tilashi cikin Daular Imam Mahadi (as) ba a tilasa mutane saboda wasu suna cewa shaidan da biyewa son yana wanze har a lokacin daular, shin yana nufin Kenan sabo zai kauce daga samuwa ba tareda tilasawa ba daga bangaren Imam kan sai sun bar aikata sabo?

 

Salam Alaikum

 riwayar nan da ta kawo batun cewa Imam Mahadi (as) yana dora hannun sa kan mutane shin tana nufin hankulan mutane zasu samu kammaluwa da kuma barin aikata sabo, ko kuma dai babu tilashi cikin Daular Imam Mahadi (as) ba a tilasa mutane saboda wasu suna cewa shaidan da biyewa son zuciya yana nan wanze har a lokacin daular, shin yana nufin Kenan sabo zai kauce daga samuwa ba tareda tilasawa ba daga bangaren Imam kan sai sun bar aikata sabo?

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ana sanin abu ta hanyar kufaifayu  kamalar hankula a zamanin mu ya sha banban da kamalar su a shekaru dubu da suka wuce a masalce, muna iya gane haka ta hanyar cigaban da ilimin kimiyya da fasaha ya samar to haka al’amarin zai kasance lokacin bayyanar Imamul Hujja (as) hankula zasu samu kammaluwa su bayyanar da kufaifayun kammaluwar su kari kan kari fiye da ninki arba’in, duk wanda hankalin sa ya samu kammaluwa maganar sa za ta karanta haka ma aikata sabo zai tawaya da’ar sa zata karu, kamar yanda al’amarin yake a wannan zamanin, lallai duk mai hankali baya sabawa ubangiji sakamakon da hankalin sa ba zai zakkewa ramin da yake cike da wuta ba ya jefa kansa ciki, lallai zai katange kansa daga hak, lallai duk wanda ya gne cewa junubi kazanta ne da bayi da turoso da wuta da guba mai kisa ta kaka zai zakkewa aikata shi, lallai shi mai cika alkawari ne a wurin Allah kamar yanda ya cikin kur’ani mai girma duka wanda ya aikata haka zai kasance mai tabin hankali mahaukaci,ranar kiyama za a tashe shi mai tabin hankali , abinda ya zo cikin suratul Kalam yana nuni kan hakan cikin fadinsa ta’ala:

(ما أنت بنعمة ربك بمجنون.. وإنك لعلى خلق عظيم)

Lallai kai bamai tabin hankali daga ni’imar ubangijinka٭lallai kai kana kan dabi’ar ma’abociyar girmama.

Daga dabi’a mai girma akwai da’ar ubangiji shi dukkkanin mai `da’a yana kasancewa ma’abocin hankali, shi kuma mai aikata sabo mahaukaci ne ko da kuwa ya kasance cikin sha’anin siyasa da tattalin arziki da sauran ilimummukan duniya mafi cikar sani da ilimi a zamanin sasai dai cewa cikin ilimin Allah da mandikin kur’ani shi mahaukaci ne.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2019/5/30]     Ziyara: [157]

Tura tambaya