mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Mene ne ma’anar wannan hadisi mai daraja?

Assalamu Alaikum. Assayid mai girma tambaya ta kan ma’anar wannan hadisi mai daraja: an tambayi manzon Allah (s.a.w) a ina Allah yake?

Sai ya bada amsa da cewa yana nan wurin masu karyayyun zukata.

 

Assalamu Alaikum. Assayid mai girma tambaya ta kan ma’anar wannan hadisi mai daraja: an tambayi manzon Allah (s.a.w) a ina Allah yake?

Sai ya bada amsa da cewa yana nan wurin masu karyayyun zukata.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Hakika tauhidi da Imani Allah ya ajiye su cikin halittar mutum ana kiran zuciya da halitta (fidra) duk wanda zuciyar sa ta karye ta tausasa lallai zai koma zuw aga abinda yake daga halittar sa sai ya ga Allah cikin zuciyar sa lallai shi Allah shine mai dora karyayye kashi, sai ya koma ga Allah yayi watsi da koma bayan sa saboda koma bayan sa shine wanda ya karya masa zuciya ta kaka zai nemi mafaka gareshi, sai ya zama baya ganin wani da zai iya dora masa karyewar face Allah girmansa ya girmama, misalin wannan ma’ana ta zo cikin wani hadisi lokacin aka tambayi Imam Sadik (as) yace masa: ka shiryar da ni zuwa ga ubangiji na sai yace: shi ka taba hawa jirgi sannan idan wannan jirgi ya karye kuma ka kasance a inda barin katakon jirgin tsakanin mutuwa da rayuwa sannan babu kowa cikin kogin in banda kai, shin a wannan halin zuciyar ka yana komawa zuwa ga wand azai tseratar da kai ya kasance kana fatan rayuwa, sai yace eh, sai Imam yace: wannan shine ubanginka da zai ceceka, wannan shine abinda ake kira da dalilin halitta kan tabbatar da dayantar mahalicci girman say a girmama.

Allah ne abin neman taimako.

Tarihi: [2019/6/9]     Ziyara: [127]

Tura tambaya