mauro,i daban-daban Taambayoyin karshe Wasu daga cikin tambayoyi Tambayoyin da akafi karantawa

Shin wadannan nassoshin sun inganta cikin kulla igiyar aureوَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ.

Daga cikin ayoyinsa aya halittar muku da mataye daga gareku domin ku samu nutsuwa zuwa garesu sannan ya sanya kauna da jin kai tsakaninku hakika cikin hakan akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani

وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ.

Daga cikin ayoyinsa aya halittar muku da mataye daga gareku domin ku samu nutsuwa zuwa garesu sannan ya sanya kauna da jin kai tsakaninku hakika cikin hakan akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani.

 

Sadakallahul Aliyul Azim.

Wasikar yarjejeniyar aure:

Daga cikin wadannan sharudda da za su zo yanzu shin ya cancantu a kulla igiyar aure da unwani awwali na fikhu ko kuma da unwanul sanawi bisa fatan zata dauki nauyin warware wasu ba’arin matsalolin zamantakewa wadanda cibiyoyi da jagororin addini suke fuskantarsu a kasashen yammaci, ni da wacce zan aura mun yarda mu ka kasance miji da mata kan sunnar Allah da Manzonsa da iyalansa tsarkaka amincin Allah ya kara tabbata gareshi tareda su baki daya.

 

1-Babu wani tilastawa tsakaninmu a cikin wannan aure.

2- ni miji wane…. Ina neman ki ke mata ta da ki tsaya kan wajibanki a matsayinki na matar da nake aure a karkashin dokokin fikhu da Aklak da karfin da Allah ya baki.

3-ni matar da zaka aura ina nema daga gareka kai mijin da zan aura da ka tsaya da dukkanin wajibai da wazifofin da suka rataya a wuyanka karkashin dokokin fikhu da Aklak da karfi da ikon da Allah ya baka.

4- mu biyu mta da miji mun dauki alkawali gaban Allah da cewa zamu tarbiyantar da `ya`yenmu kan koyarwar muslunci wacce muka sameta daga Manzon Allah da iyalansa tsarkaka amincin Allah ya tabbata gareshi tareda su.

5- mu biyu mata da miji mun dauki alkawali da cewa zamu dinga komawa ga hukunce-hukuncen muslunci da suke bayyane cikin komawa ga fatawowin Maraji’an taklidi a duk lokacin da muka samu sabani ko yanke shawarar rabuwa da juna daga kotun gari, idan ta nemi sakinta lallai ni a miji zan goyi bayan mas’alar ta nahiyar gyara da zartar da saki ya zuwa Hauzar Imam Mahadi da take birnin Baminham cikin halin tuntubar da Hauzar za ta yi da dayan daga cikin Maraji’ai masu girma.

6- lallai ju ma’aurata ne zamu yi riko da wadannan sharudda ba kuma zamu janye daga garesu cikin kowanne irin hali face da izinin Hauzar Imam Mahadi ko umarni Hakimul Shar’i.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

 

1-sharadi na daya babu laifi cikinsa

2- sharadi na biyu babu matsala.

3- na uku ma haka

4-shima babu laifi

5-babu laifi cikinsa.

6- sharadi na shida dole ya kasance daga abinda shari’a ta halasta shi, shi saki ya hannun wanda yake hannunsa ma’ana miji.

7-magana ta karshe su sharudda idan sun kasance cikin kulla aure to lazimtarsu wajibi ne sai dai idan sun kasance gabanin daura aure ko bayansa a wannan sura mustahabbine lazimtarsu.

Tarihi: [2019/7/9]     Ziyara: [151]

Tura tambaya